RABE-RABEN MASANA NA’URA
…matakan zama ƙwararren masanin na’ura
Saboda yawan kuskure ma’anonin matakan ƙwarewa a fannin na’ura ya sa na ɗauki ƙudirin yin wannan taƙaitaccen rubutun don fayyace rabe-raben masana na’ura kamar haka:
1. COMPUTER LITERACY
Mataki na farko a duniyar na’ura shi ne saninta; wato dole mutum ya san mece ce ita, yaya ake amfani da ita, da kuma yadda ake sarrafa ta. Duk wanda ya iya wannan shi ake ƙira Computer Literate. Irin waɗannan su suka fi yawa a cikin al’umma, misalin irinsu akwai masu tura waƙa da sauran al’ummar gari masu amfani da na’ura.
2. COMPUTER GEEKINESS
Idan mutum ya san na’ura da yadda ake amfani da ita da yadda zai warware matsalolinta, to yana wannan matakin, ana ƙiran shi Computer Guru ko Computer Geek. Irin su ne masu gyaran na’ura da warware matsalolinta.
3. COMPUTER SPECIALISM
Mataki na uku shi ne ƙwarewa a wani ɓangaren zamani na na’ura. A nan mutum zai ƙware a wani fanni, misali a programming, ko software development, ko häcking, ko graphics, ko embedded systems, ko robotics, da sauransu. Duk wani wanda ya ƙware a fanni guda na na’ura a wannan matakin yake, ana ƙiran shi IT Guy ko Computer Specialist.
4. COMPUTER PIONEERING
Mataki na ƙarshe kuma shi ne zama Computer Pioneer, wato wanda ya tumbatsa a duniyar na’ura har ya ƙirƙiro wani sabon abu. Misalin irinsu akwai Tim-Berner Lee, Steve Jobs, Alan Turing, Charles Babbage, James Gosling da sauransu.
A wannan bayanin za mu fahimci cewa, a misalance kamar haka abun yake:
—Computer Literate shi ne ɗan primary zuwa secondary
—Computer Guru shi ne mai digiri (BSc)
—Computer Specialist shi ne mai MSc
—Computer Pioneer shi ne mai PhD har ya zama Professor Emeritus
Wannan misali ne yadda za mu ga abun a zahiri. Don haka yana da kyau mu fahimci waɗannan matakan, don mu ma mu san matakin da muke sai mu ƙara dagewa.
Allah Ya taimaka Ya sa mu dace, amin
—Muhammad Auwal Ahmad (#Mohiddeen)
Scientist, technologist, Cofounder/CEO of Flowdiary
25th June 2022
Leave a Reply