Takaitaccen Tarihin Imam Al-Nawawi (Yahya ibn Sharaf al-Nawawi)
Manyan malamai da salihan bayin da suka gabata na iya zama babban misali ga masu rai na yanzu. Halinsu da ayyukansu na iya yin tasiri sosai a cikin zukata.
Imam Al Nawawi, wanda aka fi sani da Imam Nawawi ko Imam An Nawawi, ya rayu tsawon shekaru 44 ko 45, amma a cikin wannan kankanin lokacin, ya rubuta littafai masu tarin yawa a kan batutuwa daban-daban, kuma an san kowane littafinsa a matsayin taska mai kima na ilimin addinin Musulunci.
Haihuwarsa da Iyalinsa:
An haifi Imam An-Nawawi ne a watan Muharram shekara ta 631 bayan hijira (1233 AD) a kauyen Nawa da ke kusa da babban birnin Damascus na kasar Siriya. Al Nawawi bai fito daga sanannen dangi ba. Babu tarihin mahaifinsa da sauran danginsa. Wannan yana nuna cewa su dangi ne masu tawali’u. Duk da haka, mahaifinsa ya yi suna da kasancewa mai yawan ibada da tsoron Allah.
Cikakken sunansa Abu Zakaria Mohi-ud-din Yahya dan Sharaf An-Nawawi dan Murry bin Hassan dan Hussain dan Muhammad dan Juma dan Hazam. An ba shi suna Al Nawawi saboda sunan garinsu.
Musulunci a Karni na Bakwai Hijira (7th AH):
Karni na 7 na Musulunci lokaci ne mai cike da tashin hankali yayin da Mongols suka mamaye kasashen musulmi (A gabas ta tsakiya). Duk da haka a cikin shekaru goma na ƙarshe na karni, anci nasara akan Mongols tare da kawar da su daga waɗannan ƙasashen musulmi. Cikin falalar Allah da rahamarSa, wadannan lokuttan tashin hankali ba su kawo karshen karatun Addinin Musulunci ga mazauna yankin ba. Hasali ma, Noor AlDeen Zanki ya bude Darul-Hadith ta farko a Damascus a wannan karnin. Mutum ba zai sami karancin malamai da koyo ko da a wancan karnin na tarihin Musulunci mai cike da rudani.
Yarintarsa:
Tun yana matashi Al-Nawawi baya sha’awar wasanni. Lallai sauran yaran sun zage shi akan haka. Tun yana karami ya maida hankalinsa ga karatunsa. Ya kyamaci duk wani aiki da zai dauke shi daga haddar Alqur’ani. Wani lokaci yaran suka tilasta masa wasa da su, sai ya yi kuka saboda lokacin da yake bata wa. Don haka ba mamaki ya haddace Alqur’ani tun yana karami.
Malaminsa na Nawa ya isar da wannan lamari ga mahaifin Imam, wanda ya kasance mutum ne nagari kuma mai tsoron Allah. Da ya lura da son neman ilimin dansa, sai ya yanke shawarar sadaukar da rayuwar dansa don hidima da inganta harkar Musulunci. A cikin kankanin lokaci, An-Nawawi ya koyi karatun Alqur’ani a lokacin ya kusa balaga.
Neman Iliminsa:
Imam An-Nawawi ya rayu a Nawa yana da shekara 18 a duniya. A shekara ta 649 bayan hijira ya tafi Damascus wadda a wancan lokacin ana ganin ita ce cibiyar ilimi domin akwai cibiyoyi da kwalejoji da jami’o’i sama da dari uku a Damascus. Ya karanci Hadisi da fikihu da ka’idoji daga wajen manya manyan malaman Musulunci irin su lshaq ibn Ahmad al Maghrabi Al-Maqdisi, Abdul Rahmaan Al-Anbari, da Abdul Azeez Al-Ansaari. Ya karanta Sahihu Muslim daga Abu lshaaq Ibrahim Al-Waasiti.
Imam Nawawi ya yi karatu a makarantar Madrasah Saaramiya, Madrasah Rawahiyah (mai alaka da Jami’ar Ummvi) da Daarul-Hadits. Ya fara koyarwa a makarantar Ashrafiya yana dan shekara 24.
Sunansa da daukakarsa da matsayinsa na malami ya fara samun karbuwa a wajen malamai da mazauna birnin Damascus. A wannan lokacin ya yi aikin hajji a shekara ta 1253 miladiyya.
Neman ilimi ya mamaye rayuwarsa gaba ɗaya. Ya sanya duk lokacinsa a cikin karatu, koyo da koyarwa. Har ma an ce ba zai yi barci ba sai lokacin da barci ya kama shi. Ya d’an huta akan littafinsa ya dan yi barci, sannan ya yi firgigit ya farka ya ci gaba da karatu. Ya taba cewa game da kansa.
Na shafe shekaru biyu ba tare da na kwanta don (bacci) ba.
Al-Qutb Al-Yauneeni ya ce game da shi.
“Ba zai ɓata lokaci ko dare ba sai dai ya shagaltu da neman ilimi, ko da ya ke tafiya a tituna ya shagaltu da bitar abin da ya tuna da bitar bayanansa, ya ci gaba da samun ilimi ta haka har tsawon shekaru shida”.
Halinsa:
Ya yi rayuwa mai cike da wahala, mai sauƙi da tawali’u, ko da yake ba zai yiwu ya rayu in ba irin haka ba, idan aka yi la’akari da matsayinsa na koyarwa da tasiri. Wasu ruwayoyin sun nuna cewa, tufafin da ya mallaka, rawani ne da doguwar riga kadai. Ba ya son wani abin jin daɗin duniya. Wani lokaci baya cin komai sai waina da zaitun da mahaifinsa ke aiko masa lokaci zuwa lokaci daga Nawa. Daya daga cikin dalilan haka shi ne, yana da yakinin cewa irin wannan abinci ya zo daga halal.
Bai karbi alawus din koyarwarsa ba. Abin da Nawawi ya mallaka a duniyar nan shi ne littattafai a ƙaramin ɗakinsa. Dakinsa ya kasance kamar ɗakin ajiyar littattafai kuma burinsa ba kawai ya mallaki babban ɗakin karatu ba ne. Littattafansa ba na ado ko nunawa ba ne. Maimakon haka, ya amfana sosai daga waɗannan ayyuka daga laccoci da rubuce-rubucensa, mutane da yawa sun amfana da su tun lokacin.
Al-Nawawi Bai Taba Aure ba:
Al Nawawi bai taba yin aure ba, dalilan da suka sa hakan kuwa shi ne kaddara da rashin son jin dadin duniya. Rayuwarsa ta cika da sha’awar koyo, koyarwa da shiga ayyukan ibada. Al-Diqr ya rubuta cewa :
“Ta yiwu bai yi aure ba saboda yana tsoron ba zai iya biyan hakkin matarsa ba, saboda sha’awar karatunsa.”
Rubuce-rubucensa/Littattafansa:
Al Nawawi ya fara rubutawa ne a shekara ta 663 ko 664. Don haka a tsawon shekaru goma sha biyu ko goma sha uku ya tsara wasu muhimman ayyuka a tarihin Musulunci. Aikin sa na al’ada, shi ne, AlMajmoo, wanda bai kammala ba, an buga shi cikin manyan kundila tara. Ga kadan daga cikin ayyukansa da ya kammala cikin kankanin lokaci:
1. Riyaadh Al-Saaliheen (“Gards of the Righteous”).
2. Al Minhaj bi Sharh Sahih Muslim (Sharhin Sahih Muslim).
3. Al-Majmuu Sharh Al-Muhaddhab
4. Minhaaj Al-Taalibeen
5. Tahdhib Al-Asma wal-Lughat
6. Taqrib Al-Taisir
7. Hadisai arba’in (Arba’una Hadith)
8. Kitab Al-Adkar
9. Sharh Sunan Abu Dawood
10. Sharh Sahihul Bukhari
11. Mukhtasar At-Tirmidhi
12. Tabaqat Ash-Shafiiyah
13. Rawdhat Al-Talibeen
14. Bustan Al-Arifin
Dalibansa:
Bayan rubuce-rubucensa, ba shakka, Al-Nawawi ya yi tasiri a kan ɗalibai da yawa. Ya yi shekaru da yawa yana koyarwa kuma mutane da yawa sun amfana da shi. Wasu daga cikin sanannun ɗalibansa sun haɗa da:
1. Ibnul Attar
2. Jamaal Al-Deen al-Mizzi
3. Abu Al-abbas bn Fara’ah
4. Al-Badar Muhammad ibn Jamaah
5. Abu Al-Rabi Al-Haashimi
Al-Nawawi da Shugabannin
Shugaban musulmi a tsawon rayuwar Al-Nawawi shi ne Al-Sultan al-Dhaahir. Jarumi ne a fagen yaki. Shi ne wanda ya yaki Mongols kuma ya yi musu babban kaye. Sai dai matsayinsa da shahararsa bai hana Al-Nawawi tsayawa gare shi ba a lokacin da ya yi kuskure. Fiye da lokaci guda Al-Nawawi ko dai ya tunkari mai mulki a zauren shari’a ko kuma ya aika masa da wasiku dangane da wani lamari da ya shafi al’ummar Damascus. A wani lokaci Al-Nawawi ya aika wa Sarkin Musulmi takarda a madadin al’ummar Musulmi. Haka kuma wasu malamai da dama ne suka sanya wa hannu.
Asali dai wannan wasika wata bukata ce daga Imam Al-Nawawi ga mai mulki da ya rage harajin da ake dorawa mazauna Sham. Manufar wasikar Al-Nawawi ita ce gyara kuskuren da mai mulki ke yi. Bai sunkuyar kai ga mai mulki ba don kawai shi ne mai mulki da kuma don kawai ya yi wasu kyawawan ayyuka a baya. Duk da haka, ya gane cewa dole ne ya shawarci mai mulki. A cikin wani martani, mai mulkin ya yi iƙirarin cewa yana buƙatar karɓar waɗannan haraji don jihadi.
A ci gaba da ganawa da mai mulki ta hanyar wasiƙu da lallashinsa na yin kira ga mai mulki saboda wasu dalilai masu kyau, mai mulki ya ji haushin Al-Nawawi. Saboda haka, ya yanke shawarar a kore shi daga Dimashƙu. Al-Nawawi ya ce zai yi biyayya. Don haka ya bar Dimashƙu ya tafi garinsu Nawa. Malamai na wancan lokacin sun yi kokarin mayar da Al-Nawawi zuwa Damascus. Sai dai ya ki. Ya ce ba zai shiga Damascus ba idan Al-Dhaahir yana nan. Bayan ‘yan watanni, Sultan Al-Dhaahir Baibars ya rasu.
Ana iya cewa Al-Nawawi ya kasance mai kare talakawa, mai kare malamai kuma mai kare gaskiya. Zai yi gaba da duk wanda ya sabawa Alqur’ani da Sunna. Ba kawai yana hamayya da ƙananan mutane bane, ya bar masu iko su kaɗai. Hakazalika, rayuwarsa ba kawai ta tsaya wa mai mulki ba ne kuma ya manta da muguntar da wasu suka yi ba. Lallai ne ya sanya a cikin ayyukansa na tabbatar da alheri da kawar da munana a dimbin rubuce-rubucen da yake da su a kan bidi’o’i daban-daban da talakawan zamaninsa suka yi.
Mutuwarsa:
Bayan ya koma garinsu Nawa, Al-Nawawi ya kamu da rashin lafiya kuma ya rasu. Ya rasu a ranar 24 ga watan Rajab shekara ta 676 bayan hijira (1277 miladiyya). Ya rasu yana da shekaru arba’in da hudu.
Lokacin da labarin mutuwarsa ya kai Dimashƙu, mutane suka yi baƙin ciki ƙwarai. Hawaye suka zubo daga idanunsu. Suna cewa daya daga cikin manyan malamai kuma manyan jagororin mutane ya rasu.
Wurin Jana’izarsa:
An binne shi a garinsu Nawa na kasar Siriya. Al-Nawawi ya yi fatan cewa kabarinsa ya kasance bisa yadda Sunna ta tsara, wato a daidaita shi ba a bayyana shi ba. Duk da haka, wasu mutane sun yanke shawarar gina kubba a kan kabarinsa. Duk da haka, Allah ya cika burin Al Nawawi. A duk lokacin da suka yi kokarin gina wani abu a kan kabarinsa sai ya ruguje.
Bayan an yi yunƙuri da yawa, daga ƙarshe aka bar shi a haka dole, amma an ɗan yi masa alama bisa ga koyarwar sunna.
Rushewar kabarin
A cikin 2015, a lokacin yakin basasar Siriya da ke gudana, ‘yan tawaye masu alaka da Al Nusra sun rushe kabarin.
Allah ya sakawa Imam Al-Nawawi akan dukkan kokarinsa da kwazonsa domin Allah.
Leave a Reply