Artificial Intelligence (AI) zai fara kashe aure. [Kwararren Masanin Computer, :Ubale Kiru]
~~~~~~
I started to lose count na adadin mazan da suke contacting dina don neman shawara akan wata matsala guda daya. Kuma dukkan su, matsalar iri daya ce, as if sun hada baki. Shi yasa naga ya dace ayi addressing matsalar on a larger platform. This is serious, and it is not a joke.
It seems availability na AI akan WhatsApp da sauran kafafen sadarwa ya sa mata sun fara amfani da AI a matsayin abokin hira, abokin shawara, da kuma mai bada mafita a lokacin damuwa. Mai kara na farko yace: duk sanda su kayi fada da matarsa sai ta rika ce masa AI yace kaza ko kaza ko kaza. Don haka ita kaza kaza. Mai kara na biyu yace, duk sanda abu ya hado shi da matarsa sai taje tanawa AI korafi. Wai meye ra’ayin AI akan abun da ya faru. Wani mai karar yace, Matar sa yanzu bata masa abu sai ta fara sharing da AI don taji ko tayi ko kar tayi. Yace abin haushi, har sirri suke da AI, sai tace “Can I share a secret with you”. Wani shi kuma yace Matarsa ta saka kan ta cikin hadari, domin idan tace taza asibiti ya kawo kudi ya bata, sai kawai ta hau AI ya bata prescription, kudin asibitin kuma sai ta rike. Sai dai ya ga an saya magani an fara sha. Yanzu haka ta samu abortion a dalilin maganin da AI yayi mata prescribing. Wannan kadanne daga cikin rahotannin da aka kawo min.
Jama’a,
Artificial Intelligence (AI) ba mutum bane. Kirkirar abu ne da dan-adam ya kirkira don saukaka ayyuka da kuma automating din su. Sannan from the experts’ point of view, yana da kyau ku sani cewa har yanzu AI is a baby, ina nufin, is not matured enough da za’a karbi duk wani bayani da ya fita daga kwakwalwar sa. Kuma yana da kyau mu sani cewa ba wani mutum bane a bayan-fage yake magana da kai a lokacin da kuke hira da AI. A’a, computer ce da aka dasawa tunani irin na dan-adam, tunanin ma kirkirarre. Kwakwalwar AI ba irin ta dan adam bace, kawai dai tana kwaikwayon brain din dan-adam ne. Sannan mu lura da wannan: ko chatGPT da ya shahara, masu shi suna rubuwa a kasan interface din cewa “ChatGPT can make mistakes. Check important info.” Wato ChatGPT yana kuskure, ku rika tantance bayanan sa.
Duk abinda aka ce bashi da natural ability na nuna tausayi, gane cutarwa, gane dai-dai da ba dai-dai ba, fahimtar yanayi ya canja, ko fahimtar lokaci ya canja, ko fahimtar natural environment, karsashi – to wannan abun zai wuya ya iya fahimtar ka kuma yayi maka adalci. Akwai journal articles da dama da suka nuna cewa yanzu haka AI yana kan samun wadancen qualities (ko abilities din don ya zama danadam) din da nayi mentioning. Amma gaskiyar magana shine, Duk abinda ba Allah ne yayi shi directly ba, dan-adam ne ya yishi ko ya sarrafa shi, to sai kaga tawaya da matsaloli akan sa. Halittar Ubangiji ce kadai take zuwa so perfect ba tare da tawaya ba. Ko me za’ayi wa AI na training, bazai taba competitive da Dan-adam ba.
Don haka kuskure ne babba, mutum ya dogara da AI don neman shawara, mafita, ko neman magani, ko makamancin sa. Kamar yadda na saba fada a rubututtukana, zaka iya amfani da AI wajen saukaka aiki, karatu, ko solving problems, amma kuskure ne ayi amfani da AI wajen samar da wata mafita. Aure ba abin wasa bane, rayuwar dan-adam ba GAME PLAYING bane balle ka dora rayuwar ka akan wani technological creation wai AI. So ina kira ga mata har ma da maza masu amfani da AI da suyi hankali, kuma su kula. Ko Sarkin Masu kasada na Duniya wato Elon Musk kullum yana campaign akan mutane kar su dauki AI a matsayin dan-adam. Mujallar PCmag tace, Akalla daga 2021 zuwa Februaryn 2024, motar Tesla mai tuka kanta da taimakon AI duga 162 sunyi crashing da mutane a ciki. Akalla mutum 17 sun rasa rayukan su a dalili accidents din.
Ina kira ga Hukumonin Shara’a da yan Majalisu, da masu kare hakkin danadam irin su Abba Hikima, AUDU BULAMA BUKARTI
Lalle ya kamata ku baiwa gobnati da Judiciary shawara da su kara fadada bincike da kuma samar da dokoki da suke da alaka da emerging and trending technologies irin su AI. Domin sooner than later, zamu fara samun cases irin su “AI-based Divorce” ko kuma “AI ne ya sake ni ba miji na ba” ko kuma “AI ne yace nayi kaza ko kaza”. Hakan zai samar da regulatory policies, advisories da kuma awareness a al’umma baki daya.
Allah ya shiga lamarin mu. Don Allah kayi tagging dan Majalisar yankin ku a comment sections.
Naku,
Muhammad Ubale Jakada Kiru
AI Researcher | Cybersecurity Expert
MCP|MCSE|MCITP|CCNA|CEH|Sec+
#MuhdKiru
Tags:
Nigerian Senate
House of Representatives, Federal Republic of Nigeria
Aminiya
BBC Hausa
Leave a Reply