BAYANI AKAN MINING. HARAM KO HALAL?

 

BAYANI AKAN MINING.
HARAM KO HALAL?

Zanyi bayanin ne cikin misali da abu ɗaya kacal.

 Rubutun zai ɗanyi tsayi, amma a daure a karanta kuma a yaɗa, zai amfanar In-sha Allahu ta’ala.

====== ========= ========

MISALI.

Ni ne nake da ploti (Babban filin) da yake ɗuke da bishiyoyin mangoron dana shuka kamar guda dubu biyar, lokacin da bishiyoyin mangoron nan suka hayayyafa suka bada ƴaƴa masu yawa sai nayi himmar zuwa na zabge ƴaƴan na kai kasuwa na siyar na samu kuɗi, to amma inda matsalar take ita ce:-

✓• Na farko.

Aikin yana da yawa sosai ta yadda ni kaɗai bazan iya kammalawa ba.

✓• Na biyu.

Ina so a tallata min mangoron nan nawa a cikin gari domin jama’ah su san irin mangoron nawa su sassaya kasantuwar duk garin babu mangoro irin nawa.

To kasantuwar waɗancan matsalolin hakan tasa dole sai na gayyato jama’ah da yawa don su tayani wannan aikin, daga nan sai nayi ta gayyato mutane akan su taho su taya ni aikin zabgar mangoron nan tare da taya ni tallata shi cikin gari, sai Jama’ah kuma suka amsa ƙira na suka yi tururuwa suka zo domin yin wannan aikin, jama’ah sun karɓi wannan aikin ne bisa sharaɗoɗi guda biyu:-

✓• Na farko, bisa sharaɗin cewa duk wanda ya zabgo kwando ɗaya na mangoron zan bashi mangoro guda hamsin.

✓• Duk wanda ya kawo mutum ɗaya domin ya taya mu aikin zan bashi mangoro guda biyar.

To bayan an kammala aikin a bisa wannan sharaɗin, da aka ƙidaya kwandunan mangoron sai aka samu kwando dubu hamsin aka samu, daga cikin kwando dubu hamsin na mangoron nan sai muka lissafa abinda zan baiwa mutanen nan da suka taya ni aiki na ware musu nasu, inda yakai kaso hamsin cikin ɗari (50%), saura kaso hamsin cikin ɗarin kuma nawa ne.

Bayan haka sai na tara su na rarraba musu haƙƙinsu da muka yi sharaɗin cewa zan basu idan sun taya ni aikin nan.

To bayan ma’aikata na sun dawo gida, sai suka fara bada labarin mangoron nan nawa a cikin gari cewa ai na noma wani mangoro mai zaƙi mai kyan gaske, gasu manya-manya kuma jajaye wadda duk garin nan babu irinsu, da jama’ar gari suka ji haka sai kowa yaje ya nemo kuɗi yayi tanadi domin ina kawo mangoron nan kasuwa su saye shi kaf.

Ni kuma da labari ya isoni cewa ga irin tanadin da jama’ar gari sukayi domin sayen mangorona, sai na kwashi kaso arba’in cikin ɗari (40%) domin shigar dashi kasuwa, kaso sittin (60%) kuma na riƙe shi abu na, daga nan kuma sai na sanya ranar da zan kai mangoro na kasuwa, kafin ranar daman ƴan kasuwa sun tanadi maƙudan kuɗaɗe domin ina kawo mangoron kasuwa su saye shi.

Da na lissafa adadin mangoron kaso arba’in ɗin nan sai na samu guda miliyan uku n

 ni kuma kafin ranar da zan kai mangoron kasuwa tazo sai na tanadi kuɗi har dala miliyan uku na ajiye, da ranar tazo na fitar da mangorona guda miliyan ukun nan sai na saka musu farashin kowane guda ɗaya zan kasa shi a kasuwa akan farashin dala ɗaya ($1/1).

Kunga kenan saka masa farashin zai yi amfani ta fuskoki guda biyu kamar haka:-

✓• Zai baiwa waɗancan mutanen da suka tayani aikin nan damar sayar da mangoron da na basu a matsayin ladan aikinsu akan farashin $1 kowane ɗaya, idan mutum ɗaya ya samu guda hamsin kenan yana da $50.

✓• Zai bada dama ga masu son sayan mangoron nawa su sayi kowane guda ɗaya akan $1 zuwa sama ko ƙasa da haka. 

TAMBAYA!

Shin wannan aikin da akayi na zabgo mangoro, kawo mangoron gida, sallamar waɗanda suka tayani aiki, har zuwa kaishi kasuwa da aka yi aka fara cin kasuwar sa HARAMUN NE?

✓• Idan eh HARAMUN ne, to me ya haramta shi?

✓• Idan ba HARAMUN bane, to tabbas mining ma ba HARAMUN bane, domin exactly haka mining yake:-

TA YAYA HAKAN YAI KAMA DA MINING?

GA AMSAR.

Zan bayar da amsar ne ta hanyar fassara bayanin da nai a sama na gonar magoron nan zuwa harkar mining a taƙaice.

✓• NA FARKO.

Bishiyoyin mangororin sune a matsayin MAINFRAME COMOUTERS da aka inventing coin ɗin da akai mining cikinsu.

Kuma dasu ake amfani wajen control ɗin aikin duk wani miner da yake mining ta hanyar cloud mining (Wato mining da waya kenan) ake conversion ɗin mining da yake ya koma validated tunda ba nodes yake mining ɗin ba.

Waɗanda suke amfani da nodes kuma su babu buƙatar sai an yi musu validation na transaction ɗinsu.

✓• NA BIYU.

Mangororin kuma sune COINS/TOKENS ɗin da ake mining ɗin.

✓•NA UKU.

 Zabgar bishiyar mangoron kuma shi ne MINING ɗin.

✓• NA HUƊU.

Waɗanda na gayyato su tayani zabgar kuma sune MINERS ɗin (Ƴan baiwa kenan).

✓• NA BIYAR.

Shelanta cewa ana zabgar mangoro a gona ta duk wanda yake so yazo yai kuma shine REFERRING

✓• NA SHIDA.

 Wasu adadin mangoro dana ƙarawa duk wanda ya kawo min mutum ɗaya domin ya taya ni zabgar mangoron kuma shi ne REFERRAL BONUS/REWARD

✓• NA BAKWAI.

Yawan ƴaƴan mangoron da mutum ɗaya ya zabgo daga bishiyar kuma shi ne POINTS da miner yake samu sakamakon mining ɗin.

✓• NA TAKWAS.

Ware kason waɗanda suka taya ni aikin, da kaso na, da kason da zan kai kasuwa kuma shi ne TOKNOMICS.

✓•NA TARA.

 Ware guda miliyan uku da nayi cewa shi zai shiga kasuwa kuma shi ne CIRCULATING SUPPLY.

✓• NA GOMA.

Ware wasu adadin da nai cewa bazan kaisu kasuwa ba kuma su ana amfani dasu ne wajen samar da liquidity da wasu abubuwa daban, ana barin sune a matsayin LIQUIDITY POOL.

✓• NA SHA ƊAYA.

Ware $3Million da nai na saka a kasuwar kuma shi ake ƙira LIQUIDITY.

✓• NA SHA BIYU.

Saka ranar da zan kai Mangoron kasuwa kuma shi ne LAUNCHING DAY, kaishi kasuwar kuma shi ne LAUNCHING ɗin coin (Fashewar ta kenan).

✓• NA SHA UKU.

Adadin mangoron da na samu a gonar kuma haɗa da abinda na baiwa mutanen da suka taya ni aikin, shi ake ƙira TOTAL/MAXIMUM SUPPLY.

✓• NA SHA HUƊU.

Farashin $1 da Mangoron ya fito dashi shi ake cewa LISITNG PRICE da PRICE FIXATION.

✓• NA SHA BIYAR.

Rarraba wa mutanen da suka tayani aikin Mangoron mangoronsu kuma shi ake cewa DISTRIBUTION a crypto currency.

Akwai abinda bai fito ba?

TO MENENE BAMBANCIN SU?

Banbancin kawai shi ne, shi na mangoron a zahiri ake yinsa, shi kuma na crypto (Coin/Token) a internet ake yinsa.

Idan wancan HARAMUN ne, to tabbas wannana ma HARAMUN ne, kuma sai ayi mana bayanin me ya haramta wancan ɗin?

Idan kuma ba HARAMUN bane shi wancan ɗin, to mining ma ba HARAMUN bane, domin duk abin ɗaya ne.

…..✍️

Ibrahim Ra’ees Abou Mous’ab 

25/11/1445 H.

02/06/2024 G.


Published on: June 8, 2024. at: 2:29 pm

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*