Nasarar yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza na hannun Hamas – Blinken
….ASALIN HOTON,REUTERS
Sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken ya bayyana cewa, idan shirin tsagaita buɗe wuta da Amurka da Majalisar Dinkin Duniya ke marawa baya bai sami nasara ba, to Hamas ce ke da alhakin hakan.
Blinken ya nanata kiransa ga Hamas da ta amince da shirin kamar yadda shugaba Biden ya bayyana kwanaki 11 da suka gabata.
Ya jaddada cewa alhakin ya rataya ne a kan shugaban Hamas, Yahya Sinwar, yana mai nuni da shi a matsayin “mutum ɗaya” da ya ɓuya can ƙarkashin ƙasa a Gaza.”
Blinken ya bayyana cewa, firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya sake jaddada aniyarsa kan shawarar shirin tsagaita wuta a tattaunawar da suka yi a birnin Kudus, duk da cewa Netanyahu bai fito fili ya amince da shirin ba kamar yadda shugaba Biden ya bayyana.
Blinken ya gano martanin Hamas ga kudurin Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya da ke goyon bayan shirin tsagaita buɗe wuta a matsayin “alamar fata,” amma ya jaddada cewa har yanzu ba a samu cikakkiyar amsa daga shugabannin Hamas a Gaza ba.
Leave a Reply