.
FASHIN JIRGIN SAMAN NAJERIYA 1993.
A Ranar Litinin, 25 ga Oktoba, 1993, a Lokacin Jimamin Soke Zaben ranar 12 ga watan Yuni, wasu matasa ‘yan Nijeriya hudu, Richard Ajibola Ogunderu, Kabir Adenuga, Benneth Oluwadaisi da Kenny Razak-Lawal, sun yi abin ba zata! Sun yi awon gaba da wani jirgin saman Najeriya Airbus A310 wanda Ya nufi Abuja Daga Lagos inda suka karkatar da shi zuwa Jamhuriyar Nijar
Lamarin ya faru ne a ranar Litinin, 25 ga Oktoba, 1993, lokacin Ernest Shonekan, wanda shi ne shugaban Najeriya Na rikon kwarya.
YADDA YA FARU
Matasan – Richard Ogunderu, Kabir Adenuga, Benneth Oluwadaisi da Kenny Rasaq-Lawal – sun shiga cikin jirgin a suna jira har sai da matukin jirgin ya sanar da cewa fasinjoji za su iya kwance bel din kujera.
A cewar wani rahoto na lamarin, kamar yadda shi kansa Ogunderu ya bayyana, suka yi wa juna alama tare da kama jirgin
Fasinjojin da ke cikin jirgin da suka hada da manyan ‘yan kasuwa da manyan jami’an gwamnati, sun shiga cikin rudani da jin wata murya daban da na matukin jirgin, da ke yi musu jawabi.
Suna cewa: “Maza da mata, wannan jirgin ya kasance karkashin kungiyar Movement for the Advancement of Democracy,” in ji muryar. “Ku kwantar da hankalinku, ba za mu cutar da ku ba. Za a gaya maku inda jirgin zai sauka da ku.
Majiyoyi masu zaman kansu sun ce shirin farko shi ne karkatar da jirgin zuwa Jamus, amma da aka gane cewa man fetur ya kare, Jirgin ya nemi ya sauka a Ndjamena na kasar Chadi domin neman mai amma aka hana shi izini, daga nan kuma ya karkata zuwa Yamai babban birnin Nijar.
Da suka sauka, maharan sun ga daruruwan jandarmomi a filin jirgin, amma kafin nan sun rabawa Fasinjoji bukatunsu inda suka yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta soke zaben 12 ga watan Yuni da ta rantsar da MKO Abiola, A Matsayin Shugaban kasa.
Sun baiwa gwamnati sa’o’i 72 domin ta biya musu bukatunsu idan ba haka ba su kona jirgin. Sai dai sun kyale fasinjoji 34 su tafi tare da rike sauran 159 daga cikinsu akwai manyan jami’an gwamnatin Najeriya.
Rundunar ‘yan sandan Nijar ba za ta iya kai hari kan jirgin da karfi ba, domin ba su san ko maharan suna da horon soji ko kuma sun mallaki ababen fashewa da za su iya tarwatsa jirgin ba.
Su hudun sun rike jirgin na Tsahon kwanaki 3, inda aka yi ta tattaunawa a kan jirgin har sai da Jandarmomi suka afkawa jirgin domin ceto fasinjojin.
Ogunderu ya ce: “Sun yi zaton barci muke yi, sai suka shiga cikin dare suka yi harbi da yawa. cikin jirgin. Ina tsammanin mutum daya ya mutu.”
Da haka aka kamomu mu hudun, hannunmu a matse mu a bayanmu yayin da aka daure mu da hannu aka kai mu gidan yari a unguwar da zafin rana ya kai digiri 55.
Jami’an Nijar sun ce maharan na dauke da bindigogi da kuma wukake.
Babu wani rauni a cikin fasinjojin da aka sako, wadanda suka hada da Rong Yiren, mataimakin shugaban kasar China, in ji ministan sufuri na Nijar, Souleye Abdouleye.
Tags: FASHIN JIRGIN SAMAN NAJERIYA 1993, Ranar Litinin, 25 Oktoba, 1993, Jimamin Soke Zaben, 12 ga Yuni, matasa ‘yan Nijeriya hudu, Richard Ajibola Ogunderu, Kabir Adenuga, Benneth Oluwadaisi, Kenny Razak-Lawal, awon gaba, jirgin saman Najeriya, Airbus A310, Abuja, Lagos, Jamhuriyar Nijar, Ernest Shonekan, shugaban Najeriya, rikon kwarya, fashewa, fasinjoji, manyan ‘yan kasuwa, manyan jami’an gwamnati, rudani, kungiyar Movement for the Advancement of Democracy, ku kwantar da hankalinku, Jamus, man fetur, Ndjamena, Chadi, Yamai, babban birnin Nijar, jandarmomi, soke zaben, MKO Abiola, Shugaban kasa, sa’o’i 72, kona jirgin, fasinjoji 34, rike sauran 159, manyan jami’an gwamnatin Najeriya, Rundunar ‘yan sandan Nijar, horon soji, ababen fashewa, kwanaki 3, tattaunawa, ceto fasinjojin, harbi, unguwar, zafin rana, digiri 55, bindigogi, wukake, Rong Yiren, mataimakin shugaban kasar China, ministan sufuri na Nijar, Souleye Abdouleye,
Leave a Reply