Harold Shipman Likitan Da Take Kashe Majiyyatan Dake Zuwa Wurin Da Neman Lafiya
Harold Frederick Shipman, Jr. Wanda aka sani da Fred Shipman , babban likitan Ingila ne kuma mai kisan kai. Ana ɗaukarsa a matsayin ɗaya daga cikin manyan masu kisan gilla a tarihin zamani, tare da kiyasin mutane 250 daya kashe. A ranar 31 ga Janairu, 2000, an sami Shipman da laifin kashe marasa lafiya goma sha biyar a ƙarƙashin kulawar sa.
An yanke masa hukuncin daurin rai da rai. Shipman ya mutu ta hanyar kashe kansa ta hanyar rataye kansa a dakinsa a gidan yari a HM Prison Wakefield , West Yorkshire , a ranar 13 ga Janairu 2004, yana da shekaru 57.
An bayyana cewa ya mutu da karfe 8:10 na safe Wata sanarwa daga ma’aikatar gidan yarin ta nuna cewa ya rataye kansa A gidan yarin ta tagar dakinsa yayi amfani da zanin gadonsa Wajen Rataye kan Nasa.
An yanke wa Shipman hukuncin daurin rai-da-rai Yana daya daga cikin fursunoni 20 a Burtaniya da aka gaya musu cewa ba za a Taba sakin su ba.
Yawanci wadanda ya kashe Mata Ne ta hanyar yi musu Allura, saboda shi ya tsani mata.
Leave a Reply