Sojoji ne suka ƙaƙaba mana Obasanjo Ba da son ranmu ya zama shugaban qasa ba- Wali

 Sojoji ne suka ƙaƙaba mana Obasanjo Ba da son ranmu ya zama shugaban qasa ba- Wali

Sojoji ne suka ƙaƙaba mana Obasanjo Ba da son ranmu ya zama shugaban qasa ba- Wali

Ɗaya daga cikin jigo a siyasar arewacin Najeriya kuma tsohon ministan harkokin waje, Ambasada Aminu Wali ya ce gabanin zaben shekarar 1999, sojojin da za su miƙa mulki ga farar hula ne suka ƙaƙaba wa ‘yan siyasa Cif Olusegun Obasanjo wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasa a wannan shekarar.
Ambasada Wali wanda yana cikin waɗanda suka kafa jam’iyyar PDP a shekarar 1998, ya ce “lokacin PDP da aka je convention a Jos a shekarar 1998, abu ne da soja ke mulki, ba a bar mu mun zaɓi abin da muke so ba.”
“Da sai a ƙyale mu mu zaɓi wanda muke so. Amma haka ba ta samu ba. Ba don shigowar soja ba, suka dan saka hannunsu, watakila da Obasanjo bai zama ɗan takara ba”.
“Kuskuren da muka yi lokacin da aka kafa PDP, babu wanda ya nemi ya tsaya zaɓe a arewa sai Atiku. Wannan kuskure ne,” in ji Wali.
Ya ƙara da cewa a yanzu babu siyasar aƙida, ‘yan siyasa kawai neman takara suke yi ido rufe, shi ya sa suke sauya sheƙa zuwa waɗansu jam’iyyun a kowanne lokaci.
Ya ce “lokacin siyasa ce ta aƙida. Ɗan PRP ba zai yarda ya tsaya takara a NPN ba amma yanzu babu aƙida”.
A cewar Ambasada Aminu Wali, lokacin jamhuriya ta biyu jam’iyya ce ke da ƙarfi ba zaɓaɓɓen shugaba na gwamnati ba, “shugaban jam’iyya ya fi gwamna ƙarfin iko a siyasa”.

Zamanin mulkin jam’iyyar APC

Tsohon ministan harkokin wajen na Najeriya ya ce jam’iyyar APC ta gaza wajen ciyar da ƙasar gaba, yana mai cewa “rayuwa a yanzu tana ƙara tsanani a kasar”.
“Ba’a taba yin kuka a Najeriya ba kamar irin wannan lokacin ƙarƙashin mulkin jam’iyyar APC,” in ji Wali.
A cewarsa “inka duba yadda rayuwar talakan Najeriya take, za ka ga cewa rayuwar ta yi ƙasa. Watakila gazawar ‘yan siyasa ne na wannan zamanin. Siyasar da aka yi a baya ba irin wannan ba ce.”
Jigon a jam’iyyar PDP ya ce “ba a taɓa samun lokacin da ake kokawa kan matsin rayuwa ba a Najeriya kamar shekarun baya-bayan nan.”

Published on: June 11, 2024. at: 8:59 pm

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*