![]() |
Sabuwar Hanyar Da Barayi Ke Kwashewa Mutane Kudi A Banki Da Ya Kamata Mu Kiyaye Sakaci Da Ita |
Read this!
SIM PUK yanzu shine tsaron da kudin ka yafi bukata.
A matsayin ka na mai Amfani da bank account
Munje bank kan ganin cewa an cire mana 30,000 a matsayin biyan bashi sannan akwai sauran 128,280. Da za,mu biya.
Se suke gaya mana an ci bashi ne a account din
Koda yake daman an sace wayar da aka ci bashin tun 01-05-2024
So the same date aka ci bashin.
Abinda ya faru shine, ɓarayin wayar sunyi amfani da code din bada rance kasancewar me wayar yana amfani da First bank, su kuma kai tsaye suke bada bashi ta USSD suka ciwo bashin kudin, wanda shi me wayar bayan ya siya wata wayar yayi Swapping Sim nasa be san duk me ya faru ba.
Yaya SIM PUK ze bada kariya ga faruwar irin wannan???
Shi SIM PUK Lambobin tsaro ne da zaka seta wa SIM naka guda 4
Sa,annan duk sanda aka kashe waya to lallai se an sanya wannan PIN din guda 4 sannan ta buɗe, wanda kuma idan akayi kuskuren wannan Lambobin sau 3 to layin ze kulle kuma ba ze bude ba, se an yi swapping.
Kaga kenan koda sun cire kayinka sun saka a wata wayar koda karamar waya ce ba zata bude ba, se an sa wannan PIN din guda 4 wanda kai kadai ka san kayanka.
Ba ta yadda zasu iya cire ma kudi ko ciyo ka bashi.
Se dai su hakura ko su kulle layin da kansu.
Leave a Reply