Bayanin Da Ya Kamata A Yiwa Game Da Crypto Currency Da Kuma Forex Trading

 Bayanin Da Ya Kamata A Yiwa Game Da Crypto Currency Da Kuma Forex Trading 

Bayanin Da Ya Kamata A Yiwa Game Da Crypto Currency Da Kuma Forex Trading
Bayanin Da Ya Kamata A Yiwa Game Da Crypto Currency Da Kuma Forex Trading  @KumuryaMedia

Ga irin bayanin daya kamata akeyiwa Malamai akan Crypto/Forex…!

Yaya za’ayiwa Malamai bayanin Leverage da Margin kafin su bada Fatawa?

Mutun ne ya taso yana da jarin N100K da yake so zai fara kasuwanci da ita, a irin yadda ƙasar tamu ta kasance yadda kuɗi suke wahala N100K bazata isa tayi masa jari ba, sai yaje wajen wani mai kuɗi a unguwar su suna da tsarin da suke bayar da bashi ga mutane, tsarin su shine;

‘konawa kake so zasu baka, zasu iya nunka maka abinda kaje dashi kana so sau 10, ko sau 20 ko sau ɗari, amma dai bazaka je babu ko sisi ba saboda su tabbatar da gaske kake so zakayi kasuwancin, haka zalika idan ka fara kasuwancin indai suka ga abin yana kyau ana samun riba zasu bar maka wannan kuɗin kaci gaba da juyawa kana samun riba. Amma da zarar ka saka wasa an fara samun asara, kuɗin ka suna lalacewa a business ɗin sai su ƙwace nasu.’

Misali, kaje musu da N100K ɗinka, sai suka nunka maka ita sau 10 kuɗin ya zama 1million, kaje ka fara kasuwanci da wannan kuɗin, akan wannan Naira Million ɗayar indai riba kake samu bazasu kula ka ba kuma zasu bar maka wannan kuɗin kaci gaba da juya shi, amma idan da kasuwar ta fara lalacewa ko ka saka wasa a wannan 1million ɗin, N100K tana sauka daga ciki sai su ƙwace abinda suka baka. 

A cikin kasuwar Crypto da Forex…

1. Margin: shine wannan N100K ɗin daka zo da ita kana so a baka bashi, wanda inda badan ita ba, baza’a ɗauki kasuwancin matsayin kasuwanci ba, mutin ko bashi dako sisi kuma bai iya ba zaizo yace ya iya wannan kasuwancin yana son a bashi bashi. Da turanci suna kiransa da ‘Fair Deposit’.

2. Leverage: Kaida kazo da N100K aka nunka maka wannan kuɗin zuwa N1M, kaga ratio ɗin a lissafi zamu ce 1:10, wannan ratio ɗin shine ake cewa Leverage.

3. Exchange/Broker/Dealer: Wannan da suka nunka maka kuɗinka x10, ko x20 su muke kira da Broker/Exchange. 

Nayi karatu lessons har guda 500 a wata babbar makaranta a duniya akan Forex game da yadda abubuwa irin wannan suke faruwa, zaka iske abinda ake faɗima a social media game da abu, galibi ba hakan yake ba.

Na kanyi shiru kan wasu abubuwa na barwa kaina saboda kar ya jawo rikici, amma ko haramcin Forex da ake cewa kan Leverage da Margin ne danayi karatu mai zurfi akai, nafi ganin haramcin sa akan saboda ana trading contract ne ba ainihin kuɗin bane kamar yadda yake a spot na Crypto ko a zahiri, haka zalika haramcin futures nafi ganin ƙarfin haramcin akan saboda ana trading ɗinsa against future ne, ba akan saboda ana trading ɗinsa da margin ko Leverage ba!!!

Duk wanda bazai iya bayani dalla-dalla ga malamai haka ba ya basu misalai da yadda abin yake a zahiri, bai kamata ya zauna yanawa malamai bayanin yadda Crypto ko Forex take aiki ba, ayi adalci wajen musu bayani, sai su bamu fatawa, mukuma zamu amsa hannu-bibbiyu In shaa Allahu. Ko cikin ƴan Crypto 80% bazasu iya maka bayanin abubuwa masu sarƙaƙiya haka ba, ballantana wanda basa ciki.


Published on: June 4, 2024. at: 8:30 pm

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*