Abinda Ya Kamata Ka Sani Kan Datar Da Kake Saya Kake Hawa Internet Facebook, Twitter, WhatsApp Da Ita Ina Take Tafiya Har Ta Qare

 

Abinda Ya Kamata Ka Sani Kan Datar Da Kake Saya Kake Hawa Internet Facebook, Twitter, WhatsApp Da Ita Ina Take Tafiya Har Ta Qare

Abinda Ya Kamata Ka Sani Kan Datar Da Kake Saya Kake Hawa Internet Facebook, Twitter, WhatsApp Da Ita Ina Take Tafiya Har Ta Qare

Idan fa ka sayi data, kudin hannun kamfanin da ka sayi datar yake tafiya kamar Airtel ko MTN. Facebook, Whatsapp ko applications din mining ba abin da za su samu daga kudin datarka. 

To ta ina Facebook yake samun kudi? Ta hanyoyi manya guda biyu. Tallace-tallace (advertisement) da kuma abin da ake kira da “data brokering”. 

Duk lokacin da ka ke rubutu, ko saka bidiyo, ko saka location dinka, da sauran bayanai, to yana tafiya ma’adanar kamfanin Facebook ne su hadu su bayar da bayanai da yawa akanka. Wannan shi ake kira da “big data”. Data a nan tana nufin bayananka ba wai “data bundle” da ka siya a MTN ba.

Wannan bayanan naka ana siyar da shi a kasuwar bayanai, wacce ita ake kira da “data brokering”. Su kuma suna amfani da ita guri-guri, kamar tallace-tallace ko wani bincike da sauransu. Wani lokacin sukan siyarwa da yan siyasa don su samu damar juya tunaninka ba ka sani ba. Wannan illar ita aka gano wani kamfani mai suna Cambridge Analytica sun yi amfani da ita a wajen 2016.

Kamar yadda yan siyasa kan iya biyan “influencers” domin su juya maka ra’ayi, haka sukan je kamfanonin nan su sayi bayananka domin su gano me ya fi damunka da kuma meye burinka don su san ta yaya za su iya juyaka ba tare da ka sani ba. Wannan abin kuwa applications da yawa suna yi ba wai sai iya Facebook ko Twitter ba.

– Aliyu Dahiru Aliyu


Published on: June 3, 2024. at: 4:37 pm

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*