TASIRIN MATA 'ƳAN FILM A ZUCIYAR MAZA!!!

 TASIRIN MATA ‘ƳAN FILM A ZUCIYAR MAZA!!!

Abbas Adamu ✍️

Wani matashi ne da auren sa ya kamu da tsananin Sha’awar wata fitacciyar ‘Ƴar Film kuma ba shi da kuɗi domin shima a ƙarƙashin wani mai attajiri yake

Haka ya dinga bibiyar ‘Ƴar Film ɗin nan har ya haɗu da wani kawalinta ya yi masa magana sai kawalin ya ce ai magana ce ta kuɗi in yazo da kuɗi ba shi da matsala

Ana nan sai mai gidan yaron nan ya saka ɓasa kuɗi a account ya aike shi da su shi kuma yaron yana ganin haka sai ya ce dama ta samu nan ya kira kawalin ‘Ƴar Film ɗin nan ya ce masa kuɗi sun samu

Bayan sun haɗu da kawalin sai aka kira ‘Ƴar Film ɗin sai ta ce bata gari nan aka saka mata kuɗi suka ce ta hau jirgi tazo suna jiranta bayan ta zo sai ya sallami kawalin ya biya shi sannan ya kama ɗaki a Hotel ya kashe wayoyinsa haka ‘Ƴar Film ɗin nan tai ta kwana a gurinsa har kuɗin suka ƙare

Mai gidan yaron ya yi ta nemasa a waya amma bai same shi ba bayan yaron ya gama kashe kuɗin sai ya dawo nan mai gidansa ya nemi yaron ya dawo masa da kuɗinsa tunda bai je aiken ba

Haka dai babu kuɗi sai kame kame yaron yake yi sai mai gidan ya shigar da ƙara gurin Jami’an tsaro anan ne yaron ya faɗi yadda ya kashe ƙuɗin daga nan sai aka kai shi kotu alƙali kuma ya tura shi gidan kurkuku

Kun ji Illar bin Son Zuciya da irin tasirin da ‘Yan Film suke cikin al’ummah 

Allah Ya kyauta, Ya tsare mu bin son Zuciya da zigar Iblis.


Published on: May 30, 2024. at: 10:49 am

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*