Qasashen Spain, Ireland Da Norway Sun Amince A Kafa Qasar Palestine A Sati Mai Zuwa

 Qasashen Spain, Ireland Da Norway Sun Amince A Kafa Qasar Palestine A Sati Mai Zuwa

Ma’aikatar wajen Falasɗinawa ta yi maraba da matakin ƙasashe uku

Ma’aikatar wajen Falasɗinawa ta yi maraba da matakin ƙasashe uku
Ma’aikatar harkokin wajen Falasɗinawa ta yi maraba da matakin ƙasashen Spain, Norway da Ireland suka ɗauka na amincewa da yankin Falasɗinawa a matsayin ƙasa mai cin gashin kai.
Cikin wata sanarwa da ma’aikatar ta fitar, ta ce ”wannan muhimmin mataki ne, kuma abin as yaba ne, ƙasashenn Norway da Ireland da kuma Spain sun nuna buƙatarsu na samun kafuwar ƙasashe biyu a matsayin hanyar masalaha domin yi wa Falasɗinawa adalci”.
“Haka kuma ,matakin da ƙasashen uku suka ɗauka ya yi daidai da dokokin duniya da na Majalisar Dinkin Duniya, wanda kuma hakan zai taimaka wajen kawo ƙarshen mamayar da Isra’ila ke yi wa yankunan Falasɗinawa domin wanzar da zaman lafiya a yankin.”
Sanarwar ta kuma buƙaci ƙasashen uku da su gaggauta ɗaukar wannan mataki da suka amince da shi.

Published on: May 22, 2024. at: 5:10 pm

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*