MAZAN JIYA
Littafi Na Daya (1)
Part A
Marubuci: Abdulaziz Sani M/Gini
Typing: Abubakar Saleh AlQuyraemey
A wani zamani can baya mai tsawo da ya shude a cikin daular larabawa anyi wata kasaitacciyar kasa mai suna DARUL MAHABUR. Kasar Darul Mahabur na da matuqar girma da fadi kuma ta qunshi manyan birane a karkashin mulkin sarki guda daya mai sun MAHARAZ IBN SULEDENI.
Birnin darul mahabur ya bunqasa da karfin arziki, yawan alumma da kuma kasuwanci har ya zama abin kwatance a ko ina cikin duniya. Sarki
Maharaz ya kasance mutum mai tausayi, taimako da jin kan al’umar sa, Allah ya hore masa arziki mai dunbin yawa gami da kaifin hankali da kuma hasashen gaba yana da matar aure guda daya kacal mai suna SHALIFAT kuma basu sami haihuwa ba sai bayan shekara 11 da yin aure don haka a yanzu ‘yar su qaramar yarinya ce ‘yar shekara 8 a duniya wadda ta kasance kyakkyawa ta gaban kwatance ana kiranta da suna MULAIFA.
Tun daga lokacin da Allah ya baiwa Maharaz da Shalifata Mulaifa sai suka dauki soyaiyar duniya suka dora akanta ya zamana ko quda basa son suga ya sauka a kanta.tun da mulaifa ta taso ake tsantseni da ita kuma komai sai dai ayi mata koda ruwa zata sha sai dai a bata a baki batun jin dadi dai da hutu masana sunyi bincike sun tabbatar da cewa a wannan zamani babu ‘yar gata kamar mulaifa ko kadan sarki maharaz bai kasance Sadauki ba hasalima bai ta6a yin yaqi ba, amma yana da Sarki yakk wanda ake kira HIBRU IBN IMLAS.
Hibru ya kasance babban masoyin sarki maharaz wanda a koyaushe a shirye yake da ya sadaukar da rayuwar sa don kare ta sarki da mutuncin sarki. Sai dai wani abin mamaki shi ne duk irin wannan kauna da Hibru ke nunawa sarki tazama a banza don sarki yaqi yaja shi a jikinsa.Sharifa matar sarki maharaz ta sha yi masa fadan akan sabo da me yaki yaja hibru a jikinsa amma bai ta6a gaya mata dalili ba.sun sha samun sa6ani akan hakan har ma rai ya 6aci, akwai ranar da ta harzuqa sarki baisan sa.adda ya mare ta ba.
Cikin tsananin mamaki sharifat ta ruqe kuncinta ta dubeshi a lokacin da qwalla ya cika idanunta tace “Ya kai mijina kayi sani cewa 2n da ka aureni baka ta6a gayamin baqar magana ba bare zagi,amma yau gashi ka mareni lallai dalilin da yasa ka mareni shine yasa baka son kowa yasan sirrin dake tsakaninka da saduki hibru, ni kuwa nayi maka alkawari komai daren dadewa sai na bincika wannan sirri na san shi”
Ko da jin wannan batu sai hankalin sarki Maharaz ya dugunzuma ya risina a gaban sharifat tamkar qaramin yaro sannan ya ce “Ya ke matata ki yafe min bisa dora tafin hannuna a kuma a lokacin bana cikin haiyacina hakan ta faru ki ina cewa tunda muka hadu ni da ke ban ta6a rokon ki alfarma ba hakane?
Cikin sanyin jiki sharifat tace “Kwarai kuwa”
Sarki ya durkusa bisa guiwoyinsa a gabanta ya rike hannayenta a lokacin da idanunsa suka ciko da kwalla sannan yace “Na roke ki don darajar iyayenki da soyaiya dake tsakanin mu da ‘yar mu kada ki binciki wannan sirri domin ubangiji darbuza ya hanani yin hakan.”
sa.adda sarki maharaz yazo nan a zancensa sai jikin sharifat ya qara yin sanyi ainun kuma ta cika da tsananin mamaki daga wannan rana bata qara yiwa sarki maganar hibru ba.
Shima sarkin yaqi sau daya ya ta6a yin aure a rayuwar sa kuma matar tasa ta sami shekara 7 da mutuwa amma ta bar masa da guda daya kyakkyawan matashi dan shekara 12 ana kiransa IMNAL.
Ya gado mahaifinsa a fagen sadaukanta har ma ana ganin cewa nan gaba idan ya girma sosai sai yafi mahaifinsa jarumtaka domin 2n yana da shekara 7 yake dakawa maza gumba a hannu.duk sa,adda za.a fita yaqi dashi ake fita kuma yana taka muhimmiyar rawa irin wacce manyan mayaqan hibru ya raina abokan gaba sai yayi zamansa ya 2ra imnal ya wakilceshi wajen dakarunsa. Hakika duniya tana da fadi take haka kuma abin cikinta yawa gareshi a can wata nahiyar daban kuma akwai wani gawurtaccem sarki mai suna Dujalu Ibn Shardud wanda ke mulkin birnin hawaruldin.
Sarki dujalu ya kasance mashahurin mayaki, sadaukin sadaukai yana iya yakar mutanen gari guda ya kashe su ya kama matansu a matsayin bayi, ya kuma kwashe dukiyar su a matsayin ganima ta wannan hanya ce ya mallaki garuruwa da yawa a qarqashin mulkinsa kuma yana tara dukiya mai qazamin yawa. Bugu da kari sarki dujalu ya kasance qasurgumin matsafi wanda babu kamar sa a nahiyar.
A lokacin da sarki dujalu ya ga ya qasaita sai yai bincike a cikin halwar tsafinsa don yasan matsayinsa a akan sauran sarakan duniya. Sai da ya kwana arba’in sannan ya kammala binciken inda hankalinsa yai ma2qar tashi ya rasa abin da ke masa dadi a duniya. Ba komai ya gani ba illa sarki maharaz shine yayi dai dai dashi komai da komai. Koda sarki dujalu yaga wadannan al.amura sai ya kamu da baqinciki ya aiyana a ransa dole ne yayi 2nanin hanyar da zai bi ya rushe daular sarki maharaz ya zamana ya kawar dashi daga doron qasa kuma ya gaje dukiyarsa da mulkinsa ya hada da nasa domin ya zama babu kamarsa a duniya. Bisa wannan dalili ne ya sake shiga halwa ta kwana saba’in don ya sami mafita. Mafitar itace dole ne ya mallaki wandansu makaman yaqi na # mazanjiya wadanda zamaninsu ya shude shekarun baya, wadanda ba a ta6a yin mayaqa tamkarsu ba,kuma ba.a ta6a samun makaman yaqi masu qarfin sihirin nas ba.
Makami na farko shine wata sihirtacciyar takobi mai suna Saiful Lujara mallakar Sadauki Hantaru na Birnin Kisra sai mashi mai suna Galilil Haras mallakar Sadauki Shaddadu na birni kufa.
Sai wata hular tsafi mai suna lamsara mallakin sadauki hulkas na birnin romaniya .
☼☼☼☼☼☼☼☼☼
Ita dai takobin saiful lujara duk abin da aka sara da ita sai ya tsage gida 2 koda dutse ne ko qarfe, kuma koda shafar jikin mu2m akayi da ita sai ya mu2 saboda mugun dafin da ya ke jikinta. A yanzu haka takobin ta na can ajiye a qarqashin tsakiyar tekun Bahar dufiya a ƙarƙashin tsaron dakarun aljanu dubu 90.
Tun bayan mutuwar Sadauki Hantaru wadannan aljanu suka dauko takobin daga gidan hantaru suka kawota tekun bahar sufiya suka ci gaba da tsaronta. Ba za su gushe akan wannan aiki ba face izuwa qarshen rayuwar su don aduniya ba su da abin bauta face wannan takobi. Tun a lokacin da bokan ya qerata mutum uku kacal za suyi amfani da ita. Yanzu mutum daya yayi amfani da ita ya bar duniya ba a san sauran mutum biyun da suka rage ba. Duk wanda ya mallaki wannan takobi har abada ba za.a cishi da yaqi ba koda zai shekara miliyan a duniya. Su kuwa wadannan aljanu guda dubu 90 an gutsuri ruhin kowannen su an sa a cikin sinadarin qarfen da akayi wannan takobi, shi ya sa suka mallaka rayuwar su a kan babu wanda ya isa ya iya rabasu da ita face yana cikin mutane 3 da ke da damar anfani da ita.
☼☼☼☼☼☼☼☼
Mashin Galilil haras mallakin Sadauki Shaddadu na Birnin Kufa, a halin yanzu yana ajiye a can wani kogon sihiri dake birnin kufa, fiye da shekara dubu tun da aka ajiye mashin ba wani mahaluki da ya sake shiga kogon.
Shi dai kogon a cikin ƙarƙashin kasa yake mutum bai isa ya ga inda kofar kogon take ba face ya zo da takobin saiful lujara wajen ita ce zata sa shi a kan hanya ta shigar da shi har cikin kogon ta bude masa kofofi 99 ya isa inda aka ajiye mashin galilil haras.
Haka kuma mashin na iya rikida ya zama abin hawan mu2m doki ko rakumi wanda ba zai gaji da tafiya ko yunwa ko kishin ruwa har kwana 40.
☼☼☼☼☼☼☼☼
Ita kuwa hular lamsara shu’umar hula ce wadda idan mutum ya sanyata yana iya ganin abin da ke gaban sa nisan tafiyar kwana 40 tamkar abin a gabansa yake, haka duk irin guguwar da akeyi ko tsananin ruwan sama ba zasu kusance shi ba. Sai dai ka ga yana tafiya amma babu su a inda yake.
Hular lamsara na ajiye a cikin wani gida na kayan tarihi da ke birnin romaniya, in da aka ajiye kayan tarihin dukkanin sarakunan birnin wadanda suka shude, babu wani tsaro akan hular amma komai hatsabibancin mutum bai isa ya dauke ta ba face ya shigo dakin dauke da mashin galilil haras.
Bayan sarki dujalu ya gama nazarin wadannan kayan yaqi na # mazanjiya sai ya cika da tsananin farin ciki yayi ta kyalkyata dariyar murna.
Kashe gari kuwa da sassafe yasa a ka shirya dakaru miliyan dubu suka kama hanya suka nufi nahiyar da tekun bahar sufiya take domin dauko takobin saiful lujara, sannan su wuce birnin kufa da birnin romaniya don dauko mashin galilil haras da hular lamsara.
*****************
A can birnin darul mahabur kuwa yau ne a ke bikin qarshen sheka na bautar gunkin darbuza.
Tunda duku-dukun safiya dakin bautar ya cika da jama.a maza da mata duk inda mutum ya hanga sai dai yaga kawunan bil’adama ne rututu babu masaka tsinke, shi dai wannan dakin bauta yana da ma2qar girma da fadi.domin ya kai girman wani garin.A duk shekara mutane na zuwa daga dukkan sauran qasashen dake nahiyar domin neman tubarraki.
Saboda haka duk shekara akwai wakilan wadan nan manyan sarakuna tara dake zuwa wadan nan dakin bauta.
A wannan rannan rana sadauki hibru da dansa imnal sunzo bautar da wuri-wuri. Ba komai ne yasa hakan ba face imnal ne ya sa matsawa hibru akan lallai su zo da wuri don su kusanci gunkin darbuza.
Maganar gaskiya ita ce ba don su kusanci darbuza bane sai don kawai yaje kusa da gimbiya mulaifa ta ganshi ya ganta. 2ni imnal ya sha alwashin cewa llai a yau ne zai furtawa mulaifa cutar da take addabar zuciyar sa tsawon shekara bakwai kuma a shirye yake ya dauki duk irin horon da za.ayi masa.
Cikin sa.a kuwa su hibru suka kusanci inda gunkin darbuza yake ya zamana tazarar da ke tsakaninsu da inda su maharaz ke zaune ba ta wuce taku biyar ba.
Gaba dayan dakin bautar tayi tsit,kuma kowa ya rufe idanunsa ya sunkuyar da kansa qas. Dama haka qa’idar dokar bautar take kuma sai an shafe a qalla sa’a guda a haka,sannan sarki maharaz zai miqe yayi bayanin jawabin da gunkin darbuza yayi masa, ma.ana ya isar da saqon darbuza ga jama.a. Dama duk shekara gunki darbuza yana bayani ne akan abubuwan da sa su faru a nahir na alheri ko na tsiya. Kua duk abin da ya fada suna faruwa ne ba a ta6a samun akasi ba. Game da abubuwan tsiyan da za su faru sai ya fadi abin da za ayi domin neman tsari ko sauqi.
A wannan lokaci da kowa ya sunkui da kansa qas kuma ya rufe ido akayi tsit ne, imnal ya dago kansa ya bude idanunsa wato ya karya dokar bauta. Kawai sai ya miqe tsaye ya tafi cikin sand’a yana tsallake mutane har isa inda gimbiya mulaifa ke zaune su biyu rak. Kawai sai imnal ya zauna daf da mulaifa ya dauki hannunsa guda ya d’ora akan nata cikin firgici mulaifa ta d’ago kai don taga wanda ya ta6a ta, koda tayi arba da imnal sai ta qura masa idanu ta qame tamkar ba ta da rai . Nan take taji ta kamu da tsananin qaunar sa bata san sa.adda ta dafa hannun sa da nata d’ayan tayi masa murmushi sannan tasa bakinta akan kunnensa tayi masa magana a cikin rad’a “tabbas kaine imnal d’an sarkin yaqi hibru”
ko da jin wannan ba2 sai mamaki ya kamashi don haka sai shima ya kara bakinsa a kunnenta yace “tabbas maganarki gaskiya ce amma ya akayi kika sanni alhalin nayi imani cewa baki ta6a ganina ba?”.
Mulaifa ta ce ansha bani labarinka a siffanta mini kamanninka. Na dade ina kwatantaka a cikin zuciyata.kamannin da nake gani a mafarkina su na gani a yanzu. Kai kuwa menene dalilin da yasa ka karya dokar bauta kazo har wajena? Shin baka tsoron sarki ya sa ayi maka horo mai tsanani?
Imnal yayi murmushi ya ce ya ke ma.abociyar kyau da kwarjini ki sani cewa zuciyar da ta kamu da begen masoyi makauniya ce kuma kurma ce. Haka zalika ba ta tsoron komai a duniya muddin za ta sadu da abin begenta. Lallai na dad’e ina begenki a zuciya ta tsawon shekaru bakwai kuma a yaune nayi alqawarin sai na furta miki ciwon zuciya ta ko da kuwa bayan nai hakan za.a tsireni nan gaban miliyoyin wannan jama.a.
Da taji wannan zance sai idanunta suka ciko da qwalla ta ce “godiya ta tabbata ga ubangiji darbuza wanda ya cusa min qaunar ka a zuciyata 2n kafin na ganka da ido na.”
ya kai masoyina ka sani daga ranar da na fara jin labarinka ni ma naji na kamu da tsananin qaunar ka kuma nima yau shekara bakwai kenan ina fama da begenka a zuciyata,bani da burin da ya kai na ganka da idanuna amma damar hakan bata samu ba sai yau.
Da yaji wannan ba2 sai ya kamu da tsananin farin ciki kuma yaji sonta ya qaru a ransa d’ari bisa d’ari, kawai sai suka rungume juna.’
a dai dai Wannan lokaci ne sarki maharaz ya d’ago kansa sama ya bud’e idanunsa sharkaf da hawaye.’
ba zatao ba tsammani sai ya ga Mulaifa da Imnal a kankame da juna. A dai dai wannan lokaci ne sarki maharaz ya dago da kansa sama ya bude idanunsa domin ya yiwa jama’a bayanin sakon darbuza, idanunsa sharkaf da hawaye.
Nima ganin yadda sarki Maharaz ya dago da jajayen idanunsa yayi matukar bani tsoro yasa na tsaya cak da typing, sai Allah Ya kaimu gobe mu cigaba.
Zan ci gaba.
Da fatan anyi sallah lafiya, sannan duk wanda yake son complete zai iya tuntubata ta wannan number 08138873799 kira ko whatsapp.
Leave a Reply