Kai-tsaye: Jami’ar Columbia ta yi barazanar korar masu zanga-zangar adawa da yaƙin Gaza
Jami’ar Columbia ta yi barazanar korar masu zanga-zangar adawa da yaƙin Gaza
Jami’ar Columbia ta yi barazanar korar ɗaliban da ke zanga-zangar adawa da hare-haren da Isra’ila take kai wa Gaza.
Jami’ar ta ce ɗaliban da ke zaman dirshan a wani ginin harabar makarantar a matsayin zanga-zangar goyon bayan Falasɗinu, na fuskantar korar daga karatunsu, saboda sun karya doka.
“Ɗaliban da suka mamaye ginin na fuskantar kora,” in ji ofishin kula da harkokin jama’a na Columbia a cikin wata sanarwa, inda ya ƙara da cewa an ba masu zanga-zangar “damar fita cikin lumana” amma a maimakon haka suka ƙi tare da kara ta’azzara lamarin.
Ana kallon wannan a matsayin keta hakkin ɗaliban da ƙoƙarin hana su faɗin albarkacin bakinsu a ƙasar da take iƙirarin kare ƴancin ɗan’adam.
2130 GMT —Mamayar da Isra’ila za ta yi a Rafah za ta zama ‘mummunan bala’in da baki ba zai iya faɗa ba’ — MDD
Babban jami’in ba da agaji na Majalisar Ɗinkin Duniya Martin Griffiths ya yi gargaɗin cewa duk da kiraye-kirayen da ƙasashen duniya ke yi wa Isra’ila na ta ƙyale birnin Rafah na kudancin Gaza, “tana dab da fara kai hare-hare ta ƙasa.”
Griffiths ya ce “Maganar gaskiya ita ce, farmakin ƙasa a Rafah babban bala’i ne da baki ba zai iya misalta shi ba. Babu wani shirin jinƙai da zai iya daƙile hakan,” in ji Griffiths, bayan da firaiministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya sha alwashin ƙaddamar da farmaki a Rafah.
Griffiths ya ce ci gaban da aka samu daga Isra’ila na kai agaji a Gaza “ba za a yi amfani da shi ba don shiryawa ko kuma tabbatar da harin da sojoji za suka kai a Rafah ba.”
Netanyahu ya yi barazanar mamaye Rafah “ba tare da la’akari da ko an cim ma yarjejeniyar sulhu kan mutanen da ake garkuwa da su ba” da suke hannun ƙungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas.
Ga dukkan alamu dai ya yi kalaman nasa ne da nufin gamsar da abokan tafiyarsa masu tsattsauran ra’ayi, amma babu tabbas ko za su yi wani tasiri kan duk wata yarjejeniya da ta kunno kai da Hamas.
“Za mu shiga Rafah kuma za mu kawar da bataliyoyin Hamas a can – tare da ko ba tare da wata yarjejeniya ba, don cim ma nasarar gaba ɗaya.”
Hamas ta ce Netanyahu ba zai cim ma komai ba idan sojojin Isra’ila suka mamaye Rafah inda Falasɗinawa sama da miliyan 1.5 suke samun mafaka daga mamayar Isra’ila da kuma kai hare-hare a wasu wurare a Gaza.
Leave a Reply