DR. IDRIS YAYI HIJIRA NE DOMIN ALLAH DA MANZON SA BA DAN TSORON WANI BA: AL HASSAN MAI LAFIYA

Dr. Idris Dutsin Tanshi yayi hijira ne saboda Allah da manzonsa:
Irin wannan hijirar ba gazawa bace, sunnah ce ta annabawan Allah.
Annabi Musa A.S yayi hijira zuwa birnin madyana lokacin da fir’auna ya shirya rundunar yaki domin a hallaka shi.
Annabi Lud A.S yayi hijira alokacin da mala’iku sukazo hallaka mutanensa.
Annabi Muhammad SAW yayi hijira zuwa birnin madina.
Ashe hijira saboda Allah da manzonsa, hijira saboda addinin muslunci ibada ce kuma sunnar annabawan Allah ce.
Dariya, zagi, ko izgili ga wanda yayi hijira domin Allah da manzonsa babban bala’i ne da musiba.
Allah yasa mugane ameen.

Published on: January 29, 2024. at: 1:32 pm

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*