Jam’iyyar PDP ta Dau Zafi Kan Sace Shugabanta, Ta Aike da Muhimmin Sako Ga Tinubu
Jam’iyyar PDP ta nuna takaicinta kan sace shugaban jam’iyyar da aka yi na jihar Legas kan hanyarsa ta dawowa daga tafiya Jam’iyyar PDP cikin wata sanarwa da ta fitar ta yi Allah wadai da yadda sace-sacen mutane ke ƙara ƙaruwa a ƙasar nan a mulkin Tinubu PDP ta buƙaci jami’an tsaro da su gaggauta ceto shugaban jam’iyyar daga hannun miyagun da suka yi garkuwa da shi
FCT, Abuja – Jam’iyyar PDP ta buƙaci a gaggauta sakin shugaban jam’iyyar reshen jihar Legas Hon. Philip Olabode Aivoji, wanda aka sace a hanyarsa ta zuwa Legas daga Ibadan, babban birnin jihar Oyo. Hakan dai na ƙunshe a wata sanarwa da sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar, Debo Ologunagba, ya fitar a ranar Asabar, 27 ga watan Janairu.
Jam’iyyar PDP ta Dau Zafi Kan Sace Shugabanta, Ta Aike da Muhimmin Sako Ga Tinubu
Leave a Reply