Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi, NDLEA, ta sanar da kama tarin wasu dimbin miyagun kwayoyi da suka kai yawan kilon dub tara da dari shida da bakwai, kamar yadda ta bayyana a ranar Alhamis 6 ga watan Disamba.
Majiyar Legit.comta ruwaito hukumar NDLEA ta bayyana cewa sun kama miyagun kwayoyin ne daga watan Janairun bana zuwa watan Nuwamba, kamar yadda kwamandan hukumar, Ibrahim Abdul ya bayyana.
A cewar kwamanda Abdul, sun kama tabar wiwi na kilo dubu daya da dari shida da casa’in da bakwai (1,697), giram ashirin da bakwai (27.7) na hodar iblis, giram 10 na heron, kilo dubu daya da dari bakwai sittin (1,760.08) na kodin.
Sauran sun hada da kilo dubu biyar da dari takwas da tamanin da shida (5,886.45) na kwayar diazepam, kilo dari da arba’in da tara (149.45) na kwayar Pentazocine, sai kilo dari uku da arba’in da uku (343.7) na kwayar Rephynol.
“Baya ga kamen da mukayi, Kotu ta yanke ma mutane casa’in da biyu (92) hukunci daban daban bayan ta kamasu da laifin safarar miyagun kwayoyi daga watan Janairu zuwa watan Nuwamba, haka zalika akwai shariu da hamsin da biyar (55) a gaban kotuna daban daban.”Inji shi.
Haka zalika Abdul ya bayyana cewa sun kama mutane dari biyar da guda biyu (502), daga cikinsu akwai maza dari hudu da casa’in da bakwai (497), sai kuma mata guda biyar (5).
Daga karshe kwamanda Abdul ya yaba da kokarin gwamnati, sa’annan ya yi kira ga iyaye, malamai, sarakunan gargajiya da suaran masu ruwa da tsaki a cikin al’umma dasu cigaba da baiwa hukumar goyon bayan daya dace don ganin sun kawo karshe shaye shaye a tsakanin al’umma.
Leave a Reply