Mummunar guguwa ta kuna kai kasar Masar

Mutum daya ya rasa ransa sakamakon wata mummunar guguwa da ta kunna kai gabartekun Iskandariyya da Dahile dake arewacin Masar.

Hukumar Kula da Yanayi ta Masar ta sanar da cewa, guguwar da ta kunna kai arewacin kasar ta janyo cikar teku.

Ana sa ran yanayin zai ci gaba har nan da ranar Juma’a.

Labaran da jaridun masar suka fitar na cewa, guguwa ta kayar da wani allon talla a Iskandariyya wanda ya danne mutane biyu tare da kashe daya da jikkata daya.

Tun daga farkon makon nan zuwa yau an samu ambaliyar ruwa a kasashen Kuwait, Saudiyya da Jordan sakamakon ruwan sama da aka samu.


Published on: December 5, 2018. at: 6:44 pm

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*