Facebook Zai Goge Live Videos Bayan Kwanaki 30 – Yadda Za Ka Guji Rashin Bidiyoyinka

 

Facebook Zai Goge Live Videos Bayan Kwanaki 30 – Yadda Za Ka Guji Rashin Bidiyoyinka
Facebook Zai Goge Live Videos Bayan Kwanaki 30 – Yadda Za Ka Guji Rashin Bidiyoyinka

Daga ranar 30 June 2025 Facebook zasu fara goge duk Live Video din da aka yi wanda ya zarce kwanaki 30. Meaning: Idan kayi Live video through Live streaming, bayan kwanaki 30 za’a goge su har abada.

   ~ Idan kana so su zauna har abada sai dai kayi saving dinsu akan Memoryn wayar ka, ko akan Google Drive. Ko ka dinga sharing dinsu a wasu Media channel din, kamar YouTube, Tiktok da sauran su.

Ko kuma kayi downloading dinsu daga Facebook sainka sake yin posting dinsa a matsayin post ba a matsayin Live Video ba.

   ~ Wannan shirme da shiriritar da Facebook zasu fara yi kenan nan da kwanaki 115 masu zuwa. Zasu goge miliyoyi ko biliyoyin videos masu tsananin amfani na ilimi, tarihi da rayuwa.

Wato duk video daka dora shi through Live streaming zasu goge shi.

So, Media team na Malaman addini ko kuma masu business ko masu dora videos masu muhimmanci game ilimin Boko ko wata harka, idan zasu yi video toh su dinga dora shi akan YouTube ko Tiktok bayan facebook.

Ko kuma a sake uploading na videon a Facebook bayan an dauke shi Live. Ko kuma idan za’a yi Live a hade su waje daya wato a lokacin da ake dauka a facebook at the same time ana yin sa a YouTube ko Tiktok.

   ~ Idan ba haka ba za’a neme su a rasa duk muhimmancin su. Allah ya kyauta, wannan shirmen ya kai shirme gaskiya.


Published on: March 6, 2025. at: 8:45 pm

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*