Shugabannin Larabawa sun amince da tsarin gina Gaza da zai laƙume dala biliyan 53
Shugabannin ƙasashen Larabawa sun amince da tsarin sake gina Gaza wanda zai lakume kuɗi da ya kai dala biliyan 53 wanda ya sha bamban da manufar Trump na son “karɓe iko da Gaza” da kuma fitar da Falasɗinawa sama da miliyan biyu daga yankin.
Sun amince da tsarin ne a wani taron gaggawa da suka gudanar a Alkahira, babban birnin Masar.
“Tsarin Masar a yanzu shi ne tsarin Larabawa,” kamar yadda sakatare-janar na ƙungiyar ƙasashen Larabawa Ahmed Aboul Gheit bayan kammala zama na tsawon sa’o’i da aka yi.
Ba tare yin magana kan manufar shugaba Trump a kan Gaza ba, ya bayyana cewa “matsayar Larabawa ita ce watsi da duk wani yunkuri na ɗaiɗaita Falasɗinawa, ko da da son su ko tilasta su”.
Masar ta fitar da wani jadawali mai shafi 91 ciki har da hotuna na yadda birnin Gaza zai kasance idan aka sake gina shi, wanda ya yi saɓani da tsarin Amurka mai suna “Sake Mayar da Gabas Ta Tsakiya” wanda ya kaɗa ƙasashen Larabawa da kuma duniya.
Abin da ya sa wannan tsari ya yi daban shi ne ba wai domin irin tsarin gine-gine da za a yi ba; akwai allunan batun siyasa da kuma ƴancin Falasɗinawa.
A jawabinsa a wajen taron, shugaban Masar Abdul Fattah al-Sisi ya yi kira da a samar da tsare-tsare guda biyu da za su tafi lokaci ɗaya wanda aka fi sani da tsarin ƙasa biyu – ƙasar Falasɗinawa da kuma ta Isra’ila. Ƙasashen Larabawa da kuma sauran mutane na ganin wannan shi ne kaɗai hanyar samar da mafita ga rikicin da aka daɗe ana fama da shi, sai dai Firaiministan Isra’ila Benjamin Netanyahu da ƙawayensa sun yi watsi da batun.
Wannan sabon tsari ya bayyana cewa Gaza za ta zauna karkashin kulawar “gwamnatin Falasɗinawa na wucin-gadi” wanda ya kunshi kwararru.
Sai dai ba su bayar da cikakkun bayanai ba kan rawar da, har ma idan akwai wanda Hamas za ta taka.
A kann batun barazanar ƙungiyoyin mayaƙa, ƙungiyar ta ce za a warware wannan matsala idan aka magance abin da yake janyo rikicin daga ɓangaren Isra’ila.
Yayin da wasu ƙasashen Larabawa ke yin kira don kawo karshen Hamas; saura kuma sun yi imanin cewa matakin haka ya rage ga Falasɗinawa. An bayyana cewa Hamas ta ce ta amince ba za ta taka wata rawa ba wajen tafiyar da Gaza, amma sun bayyana ƙarara cewa ajiye makamai ba abu ne mai yiwuwa ba.
Firaiministan Isra’ila Benjamin Netanyahu, wanda ya yaba da tsarin shugaba Trump kan Gaza, ya sha bayyana cewa Hamas ba ta da wani rawa da za ta taka, har ma da hukumomin Falasɗinawa.
Sun kuma tattauna kan batu mai muhimmanci na tsaro ta hanyar yin kira ga kwamitin tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya da ya aika dakarun wanzar da zaman lafiya.
Za a kuma gudanar da wani taron ƙasa da ƙasa a wata mai zuwa domin tara kuɗaden da ake buƙata wajen aikin sake gina Gaza.
Ƙasashen yankin Gulf masu arziki su ma sun nuna buƙatar ba da kuɗi don yin wannan aiki. Sai dai babu wanda ya shirya don ba da kuɗi har sai sun tabbatar da cewa ba za a sake ruguza gine-ginen ba a wani yaƙi.
Yarjejeniyar tsagaita wuta mai tangal-tangal wanda a yanzu ke daf da ruguje wa za ta ƙara dagula al’amura.
Wannan sabon tsarin sake gina Gaza na ƙasashen Larabawa zai wanzu a kashi uku, inda za a fara da shirin na tsawon watanni shida, wanda aka yi wa lakabi da tsarin sake mayar da asara, domin fara aikin kwashe ɓaraguzai. Sauran kashi na biyu da na uku kuma zai shafe tsawon shekaru da dama.
Yayin wannan lokaci, Falasɗinawa da aka ɗaiɗaita wanda aka yi kiyasin sun kai miliyan 1.5, za a samar musu da gidaje na wucin-gadi. Hotunan tsarin gidajen da aka fitar ya nuna yadda aka ƙawata rukunin gidajen a yankin.
Shugaba Trump ya ci gaba da tunanin “Me ya sa ba za su fice ba?” Kwatanta Gaza da wurin da ake “ruguje-ruguje” ya nuna yadda aka ruguza yankin. MDD ta ce an lalata kashi 90 na gidaje a Gaza.
An ruguza ko shafe duk wani abu na more rayuwa, kama daga makarantu da asibitoci da tsarin magudanan ruwa da kuma layukan lantarki.
Shugaba Donald Trump ya fusata da kuma kaɗa mutane lokacin da ya wallafa wani bidiyo da aka haɗa da ƙiƙirarriyar basira (AI) na yadda zirin Gaza zai kasance a karkashinsa a shafinsa na Truth Social, wanda ya nuna mutum-mutuminsa da abokinsa Elon Musk suna cin ƙwalama, da kuma shi tare da Benjamin Netanyahu suna kallon juna, babu riga a jikinsu. Suna kuma jin waƙa mai daɗi mai cewa “Gazar da Trump yake so ta iso”.
“Suna da shugaba Trump a zuciya,” a cewar wani ɗan diflomasiyyar yamma wanda ya halarci taro kan tsarin da Masar ke da shi a ma’aikatar harkokin wajen ƙasar da ke Alkahira. “An shirya abubuwa sosai.”
Masar ta bijiro da ƙwararru da dama da tsarin da take son yi, kama daga ƙwararru daga bankin duniya kan ɗorewa, zuwa masu tsara ko gina ƙayatattun otel-otel daga Dubai.
Akwai darussa da dama da aka koya daga wasu birane da aka ruguza waɗanda suka koma ɓaraguzai wanda ya kunshi Hiroshima da Beirut da kuma Berlin. Kuma tsarin da aka bijiro da shi kan Gaza – ya samu tasiri ne a wajen Masar musamman wajen gina “Sabon Alkahira” ɗin ta, wanda ya kasance wani gagarumin aiki.
Shugaban na Amurka ya ce ba zai “tilasta” manufarsa kan kowa ba, amma ya hakikance cewa tsarin sa shi ne kaɗai “yafi aiki”.
Yanzu ya rage ga ƙasashen Larabawa da kuma ƙawayensu wajen tabbatar da cewa tsarin su shi ne kaɗai yafi.
Leave a Reply