SHEIKH PANTAMI: GUZURIN RAMADAN 1: ADDU’AR GANIN WATAN RAMADAN

GUZURIN RAMADAN 1: ADDU’AR GANIN WATAN RAMADAN!
Idan aka sanar ya tabbata anga JINJIRIN WATAN RAMADHAN, ana bukatar MUSULMI ya karanta wannan addu’ar: “Allahumma ahillahu alaina shahru Ramadan bil Amni, wal Iman, wal Salaama, wal Islam, Wat Taufiq Lima tuhibbu wa tarba, Rabbuna, wa Rabbukal Laah”  
(Tirmizhiy, Shaykh Albani ya
inganta shi)
Ma’anar Adduar: Yaa Allah ka sa (wannan wata ya kasance) na samun tsaro, da Imani, da zaman lafiya, da musulunci da dacewa ga
abunda kake so, Mahallincu shine Mahaliccinka Allah.
Yaa Allah ka Bamu ikon karanta wannan addu’ah kuma ka amsa mana idan mun Karanta Yaa Allah.

Published on: March 1, 2025. at: 7:44 pm

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*