Aston Villa za ta rike Rashford, Osimhen ya matsu ya je Man Utd
![]() |
Image Source: Getty Image |
Marcus Rashford zai ci gaba da zama a Aston Villa bayan aro, yayin da Victor Osimhen ke matsa lamba don komawa Manchester United. Arsenal na shirin sayar da Trossard ko Martinelli, Chelsea da Bayern Munich na zawarcin ƴan wasa. Karanta cikakken bayani kan sabbin labaran canje-canjen ƴan wasa a duniya cikin Hausa.
Ɗan wasan gaba a Manchester United da Ingila Marcus Rashford mai shekara 27, na shirin tabbatar da zamansa na aro da ya je Aston Villa a watan Janairu zuwa zama da dindindin. (Sun – subscription required)
Barcelona da Bayern Munich sun shiga zawarci kan Rashford. (Football Insider)
Liverpool na sake nuna zakuwarta kan ɗan wasan gaba a Newcastle da Sweden, Alexander Isak, yayinda Arsenal ke nuna matsuwarta kan sayar da matashin mai shekara 25. (Times – subscription required)
Arsenal za ta bukaci sayar da ɗan wasan gaba a Belgium, Leandro Trossard mai shekara 30, ko kuma ɗan wasanta na Brazil mai shekara 23, Gabriel Martinelli domin samun kudaden sake gina ƙungiyar a lokacin bazara, dukkanin ƴanwasan na samun tayi daga Saudiyya. (Mirror)
Victor Osimhen ya matsu kan yarjejeniyar tafiya Manchester United, ko da yake sai ƙungiyar ta matsa kaimi wajen kalubalantar manyan ƙungiyoyi kan ɗan wasan mai shekara 26 daga Najeriya, da ke zaman aro a Galatasaray daga Napoli. (Teamtalk)
Manchester United ta shirya rabuwa da ɗan wasan gaba a Denmark, Rasmus Hojlund mai shekara 22, domin iya sayen Osimhen. (Calciomercato – in Italian)
Chelsea na cigaba da farautar ɗan wasan Borussia Dortmund da Jamus, Karim Adeyemi, wanda aka kiyasta kudinsa kan yuro miliyan 45. (£37.1m). (CaughtOffside)
Manchester City na kokarin sayen mai tsaron raga domin maye gurbin Ederson na Brazil mai shekara 31, ƙungiyar na tattaunawa da Porto kan ɗan wasanta na Portugal Diogo Costa. (CaughtOffside)
Bayern Munich ta janye tayinta kan ɗan wasan tsakiya a Jamus, Joshua Kimmich bayan ta ji haushi kokarin tsawaita zamansa a inda yake. (Bild – in German)
Barcelona ta nuna kwaɗayinta kan ɗan wasan AC Milan da Portugal, Rafael Leao mai shekara 25. (Nicolo Schira)
Newcastle United na farautar ɗan wasan Burnley mai tsaron raga, James Trafford, mai shekara 22. (Football Insider)
Leave a Reply