Ai an Gama Muqabala da Ɗan Antiy tun Shekaranjiya, an sameshi Har Gidan sa, Kuma anyi Nasara Akan sa, saboda Waƴannan Dalilan:
1- Ɗan Antiy yace wai ba’a sanar dashi ranarda za’a zo Wurin sa ba.
Tambaya: Ɗan Antiy yace Komai Allah ne! Kuma naga wani Video Yana zaune wasu Na ce masa shima Allah ne.
Daman shi Allah Yana buƙatan asanar dashi Wani Abu da bai Sani ba?
2- Sarkin Awe, ya aika saƙo cewa Ɗan Antiy yazo yayi baƙi, sai yace bazai iya Fitowa daga Gidan shi ba, saboda Wai bashida lafiya!
Tambaya: Daman Shi Allah Yana rashin lafiya?
3- Ɗan Antiy yace bazaiyi Muqabala ba,sai ya sanarda Magabatan sa, duk abinda sukace zaiyi bayani,sai yace saboda Magabatan sa, akaron farko basu goyon bayan yayi wannan Muqabala, da ƙyar suka yadda yayi a farko kenan!
Tambaya: Daman Allah yanada Magabata ne da har bazai iya yin wani Abu ba, sai ya nemi yardarsu Ko izinin su?
Natijar Muqabala da Ɗan Antiy:
Ta tabbata Ɗan Antiy Maƙaryaci ne, Shi ba Allah bane, saboda Allah na Gaskiya Babu Abinda bai sani ba Masanine Akan Komai,Kuma baya Rashin lafiya,Babu wani Abu da yake hanashi Ko yasashi Wani Aiki,tsaye yake dakansa Baya bukatan Komai wurin Kowa.
Aqidar Komai Allah ne, ba Gaskiya bace Zindiƙanci ce Ɗan Antiy Bayada Hujja, saboda haka an kaishi a Ƙasa ya fadi warwas.
Allah ya Sakama Su Malam Kakisu da sauran tawagar Sunnah da Alkhairi.
Leave a Reply