Sheikh Auwal Albany Zaria: Shin Da Gaske Da Hannun Saudi Arabia A Yaduwar Ta addanci Dukda Iqrarin America

Wai Albani ya ce “asalin ta’add@cin Makkah da Madinah ne (Saudiyya)?”
Na ce, an dai yi wa Albani FASSARA TA SON RAI. Ka kalli full lecture kuma ka san akan me ma malam ya yi magana? 
Eh! Malam ya ce akwai Malamai a Saudiyya da suke rubutu da goyon bayan B*KO H*RAM, waɗanda suka fi maganar su ne Prof. Al*nbari da Abdullahi Fauza*n Fauz*n. Malam yana ƙalubalantar ire-iren malaman nan ne da suke koyar da tsattsauran ra’ayi ne, har su kai ga matakin ɗaukar makamai. 
Su waɗannan mutane ne (a karan kansu) ko gwamnati ne? Masu aƙida ne a karan kansu ba kowa suke wakilta ba.
Idan irin wannan analogyn ne za ka yi, sai mu ce su Bello Turji Kachalla, Dogo Giɗe ‘yan Zamfara da yake aiyukan ta’addanci, Zamfara ce asalinsu. Hakan na nufin, gwamnatin Zamfara ce ta ƙirƙiro?
Saudiyya tana bada SCHOLARSHIP a je karatu a jami’a, a cikin malamai kuma akwai masu tsattsauran ra’ayi da suke influencing ɗalibansu, kuma mutum nawa gwamnati ta kama tana rufewa saboda haka? Mutum nawa Gwamnatin Saudi ta kama, ta daure saboda extremism? Malam ma cewa wasu Malamai, ba gwamnati ba.
Kuma ka ji, tun 1990s ma Saudi ta kori Os*ma bin Lad*n da masu irin aƙidarsa ta tsauttsaran ra’ayi, su Abdullahi Azz@m, Aym@n Al-Zaw@hiri da sauransu.
Kai! Saboda yaƙi da ta’add@nci har cibiya aka kafa a Saudi, Islamic Military Counter Terrorism Coalition (IMCTC), ga ETIDAL, MBNCCC, ga AML, TFTC, kai har da kotu ta musamman da ke hukunta wadanda aka kama da aiyukan ta’add@nci (Specialized Criminal Court).
Ita ma kanta University of Madinah (IUM) kullum cikin aiyukan tarewa da hana tsauttsauran ra’ayi take, tunda daga kan ‘curriculum’ nasu, haɗa conferences da special programs kamar yadda muke GSP jami’o’inmu, haka suke Moderation and Counter-Radicalization (MCRC), Islamic Values and Counter-Terrorism (IVCT).
Idan kuma ka ce Ibn Taymiyya yana koyar da ta’addanci saboda suna karantowa daga wallafarsa, idan kuma wata ayar Alkur’ani kuma suka karanta suka ba ta tawili daidai da son ransu fa? Ka taɓa karanta tarihin Ibn Taymiyya, ka san yadda ya rayu cikin takura, da matsi, da su ne dalilan sanya shi zafi a fatawowinsa? Shikenan don wani
Saboda wasu tsiraru sun tsaurara sai ka yi duk mutane bakin fenti? Kana zaune da ‘yan Salafiyyaa makaranta, kasuwanni, har salla kana yi a masallantansu, me ya sa ba su kashe ka ba? 
Kada kalmomin Turanci ma su ruɗar da kai, milit@ns, gunm@n, coloni@ls, duk akwai aiyukan ta’adancci cikin lamuransu. Shin Musulmai ne kawai ta’addanci? Ina RSS, KKK, FARC, Antifa… ko abin da Isr@el ke yi wa P@lestine na Nakba? Su kuma waɗanda suke yi wa Musulunci kallon addinin ta’add@nci, ba ruwan da Ɗarika ko Salafiyya, Shi’a ko sectless, duk sunanku Musulmai.
Nuhu Saad Kumurya

Published on: February 20, 2025. at: 8:14 pm

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*