Blockchain: Shin ana iya dora coin a kasuwa koda ba yardar masu shi?
Farko kafin mu amsa wannan tambayar akwai bukatar mutane su fahimchi wasu abubuwa masu matukar muhimmanchi dangane da blockchain kamar haka:
Testnet
Lokachine da ake gwada blockchain domin tabbatar da inganchinsa. Bayan devs sun kammala aikinsu na kirkirar blockchain, ba lokachi guda ake sakarwa mutane shi a kasuwa ba su fara amfani dashi, sai an samu wasu mutane sunyi aiki dashi domin tabbatar da cewa komai yayi. A matakin testnet ne ake bawa mutane damar gwada wannan blockchain din ta hanyar yin transactions daban-daban kamar swapping, bridging, staking, providing liquidity, transfer da sauransu. A yayin gwajinne idan aka gano wata matsala sai devs din su gyarata. A testnet ana amfani da coins na bogi, bana gaske ba domin gwaji. Misalin testnet shine kamar na Mango da muka kammala a yau, wanda zamuga cewa munyi amfani da coins na bogi kamar MGO, ETH, BNB domin gwada Mango Network.
Mainnet
Mainnet shine lokachin da blockchain ya zama live, ma’ana ya zama na gaske, wato mutane zasu iya amfani dashi. Za’a iya dora masa projects akansa, duk wani coin da za’ayi amfani dashi akansa na gaske ne. Mainnet ya rabu kashi hudu (4), amma wayanda mutane sukafi sani sune Close Mainnet da Open/Public Mainnet.
Close Mainnet
Close Mainnet shine lokachin da blockchain ya zama live amma kuma ana control dinsa, ma’ana dai babu decentralisation akansa. Masu blockchain din sune suke da ikon gudanar da komai akansa, wato dai wani bazai iya kirkirar project akansa ba. Misali, idan blockchain yana matakin close mainnet wani bazai iya kirkirar token, NFT, wallet, da sauransu akan wannan blockchain din ba. Duk wani project da ake son kirkira akan wannan blockchain din masu shine kadai zasu iya kirkirarsa. Atakaice dai, indai blockchain yana matakin close mainnet, babu wanda yake iya ta’ammali dashi sai masushi.
Open/Public Mainnet
Open Mainnet shine lokachin da kowa yake iya ta’ammali da blockchain koda yardar masu shi ko babu. Yana chikin alamun blockchain ya zama open mainnet shine ya kasance decentralize kuma permissionless, ma’ana dai babu mai iko dashi, kuma ba bukatar neman izini kafin ayi ta’ammali dashi.
To yanzu mu koma kan tambayarmu ta farko, wato shin ana iya dora coin a kasuwa koda babu yardar masushi? Amsar itace eh ana iya dorawa indai yana kan open/public blockchain ne, domin wannan ka’idar ta decentralisation da permissionless da open blockchains suke dashi. Daga lokachin da blockchain ya zama open mainnet to duk wani project da aka dora akansa kowa zaiyi ta’ammali dashi da yarda masu project din ko babu yardarsu.
Bari muyi gwari-gwari, har yanzu ba’a san inda Satoshi Nokomoto yake ba, amma kasancewar Bitcoin blockchain yana matakin open mainnet kowa yana ta’ammali da Bitcoin blockchain ba tareda neman yardar Satoshi ba. Hakama duk wani coin idan an kirkireshi kasuwar crypto (Dex ko Cex) sunada ikon dora coin matsawar an kirkireshi ta hanyar amfani da smart contract dinsa.
Idan yau na kirkiri blockchain, kuma ya zama open mainnet. To duk wani coin ko token dazan kirkira akansa ko kuma wani ya kirkira akan to kowa yanada ikon ta’ammali da wannan coin ko token din a fadin duniya, koda yardata ko babu. Haka zalika, exchange sunada ikon dora duk wani blockchain da ya zama open mainnet akansu, haka zalika sunada ikon dora duk wani coin da aka kirkira akan wannan blockchain din. Babu bukatar neman izini, saidai ya kasance sune zasu dora masa liquidity.
Wannan shine tsarin open blockchain: transparent, decentralize & permissionless.
Nuhu Saad Kumurya.
CEO, Co Founder of Kumurya Media Tv
Leave a Reply