Cyber Security: Abinda Yakamata Kasani Kafin Kaje Karatunsa – Hanyar Zamowa Kwararre A Cybersecurity

Cyber Security: Abinda Yakamata Kasani Kafin Kaje Karatunsa – Hanyar Zamowa Kwararre A Cybersecurity
Image Source: Facebook
Cyber Security: Abinda Yakamata Kasani Kafin Kaje Karatunsa – Hanyar Zamowa Kwararre A Cybersecurity
Image Source: Facebook

 

CYBER SECURITY: ABINDA YAKAMATA KASANI AKAN CYBER SECURITY KAFIN KAJE KARATUNSA

 

Diyawa daga cikin sabbin dalibai a wannan sahar ko kuma wanda suke son zuwa karatun Degree da zaran an ambaci Cyber Security abinda yake zuwa ƙwaƙwalwarsu shine “Hacking” wato dandantsa, to yana da kyau musani cewar a gaskiyar lamari a Cyber Security ba hacking ake koyarwa ba, sai dai ana koyarda yadda ake tsaron na’ura ne a matakai daban daban. Mai karatu biyo ni kaji bayani dalla dalla.

Ibrahim Auwal: Ya Kamata Matasan Arewa Suyi Amfani Da Kudin Da Suka Samu A Notcoin Wurin Karatu Akan Blockchain Technology

Kalmar “Cyber” na nufin fasaha da kuma abinda ya danganci na’ura mai ƙwaƙwalwa, shi kuwa “Security” na nufin tsaro, a takaice kalmar Cyber Security na nufin ilmin tsaron na’ura, idan mukayi duba a sanake bama sai amfada mana ba zamu fahimci cewar lallai babu zancen “Hacking” aciki sai wanda ba’a rasa ba. A karkashin ilmin Cyber Security ana koyarda abubuwa ne kamar haka:

 

1. Cyber Law/IT Law: ilmin sanin dokokin mu’amala da bayanai a kan Computer da kuma ka’idojin amfani da yanar gizo A cyber security.

 

2. Ethical Hacking and Penetration: A koyarda hanyoyin da masu hacking suke amfani dashi wajen kai hare harensu.

 

3. Network Security: Ilmin tsaron hanyoyin sadarwa wannan ya danganci sanin aiki da irinsu Firewall, VPN da kuma amfanin su da sauransu.

 

4. Cryptography: Fasahar boye bayanai daga asalinsa zuwa yadda dan Adam da kuma Computer baza su iya fahimtar su ba.

 

5. Information Security: Ilmin kula da Bayanai.

http://fb.me/saadnuhukumurya

6. Incident Response and Digital Forensics: Hanyoyin binciken kwakwaf na fasaha da kuma maida martani idan ankawo hari da yadda za’a iya kare kai da sauransu.

 

Wadannan sune wasu daga cikin abubuwan da ake koyarwa a wannan fannin. Sai dai yana da kyau musani ana taba programming sosai aciki musamman irinsu Web Development domin nuna maka hanyoyin hadura da kare kai.

 

Yakai mai son karatun wannan fannin ga wasu shawarwari:

 

1. Kanemi Computer: Wannan wajibi ne matukar da gaske kanaso ka kware, samun computer zai baka damar samun ilmi fiye da na iya aji da kuma fadada karatun da fiye da sauran.

 

2. Ka koyi programming ko da kadanne: Yana da kyau musani a harkar Cyber Security ba iya theory bane, lallai akwai bukatar ka iya Programming matukar kanaso kazama kwararren hacker ba Script kid ba kamar yadda muke kiran mutane a ɗa. Sanin yadda ake hada abu zai taimaka wajen fahimtar ya ake bata wannan abin. Bara in baka misali kwanaki Umar A Baba yaje zaiyi submitting wani application sai ya tarar deadline ya wuce, harma an kulle amma abinda yake faruwa shine form din yanq nan anyi Comment din submit button dinne abinka da wanda yasan abu take kwakwalwarsa ta bashi logic abinda yayi shine yayi amfani da Browsern ne yayi editing page din sannan yacire comment din akan button din kuma yayi submitting in takaice maka komai yayi dai dai, idan da wanda baisan abin ba zaiji labari da sai ya dauka wata abar akayi a wajen amma zallar dabarace.

 

Yadda a film ake nuna yadda hacking yake a zahiri ba haka bane, duk da in mun lura su film suna nuna Codes yana ta yawo hakan na nufin suma suna fadamaka lallai koyon Programming dinka yana da matukar amfani.

 

3. Kanemi kwarewa a farko: mafi girman kuskuren mutanen mu shine hango kudi tun mutum bai kware ba a abu, misali tun satin farko ya fara koyon abu zakaji yana lissafin yadda wasu sukayi kudi a fannin ko kuma salaryn da ake biya a fannin ba tare da la’akari da tsawon lokacin da ake daukawa kafin akai wannan matakin ba. Bayan karatun aji ka tabbatar ka kware a duka vangarorin da kake akai ko ince aka koyar dakai.

 

4. Kasani indai kwarewa kake bukata sai karatun ka yawuce fiye da na aji.

 

5. Indai Hacking kakeso ka kware kai da kanka zaka koya kuma sai ka dauki shekaru kafinnan.

 

– Nuhu Saad Kumurya

18/10/2024.


Published on: March 21, 2025. at: 1:33 pm

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*