Dr. Idris Dutsin Tanshi yayi hijira ne saboda Allah da manzonsa:
Irin wannan hijirar ba gazawa bace, sunnah ce ta annabawan Allah.
Annabi Musa A.S yayi hijira zuwa birnin madyana lokacin da fir’auna ya shirya rundunar yaki domin a hallaka shi.
Annabi Lud A.S yayi hijira alokacin da mala’iku sukazo hallaka mutanensa.
Annabi Muhammad SAW yayi hijira zuwa birnin madina.
Ashe hijira saboda Allah da manzonsa, hijira saboda addinin muslunci ibada ce kuma sunnar annabawan Allah ce.
Dariya, zagi, ko izgili ga wanda yayi hijira domin Allah da manzonsa babban bala’i ne da musiba.
Allah yasa mugane ameen.
Leave a Reply