
Fatima bint Al-Aswad: Musulmar Da Aka Fara Yanke Hukuncin Haddi Kan Laifin Sata

Fatima bint Al-Aswad (Musulmar da aka fara yanke mata hukuncin haddi a kan laifin sata)
Tan Nigeria Hudu Da Aka Kama Da Laifin Fashin Jirgin Sama A Nijar
Fatima bint Al-Aswad (da Larabci: فاطمة بنت الأسود ), a zamanin Annabi Muhammadu (SAWW), ita ce Musulma ta farko da ta fuskanci hukuncin haddi akan laifin sata, an datse hannunta bisa umarnin Annabi Muhammad (SAWW).
Fatima ta kasance daga dangin Makhzum na kabilar Kuraishawa a Makka. Ana kuma kiranta da Umm Amr bint Sufyan, tun da Sufyan dan Al-Aswad bn Abd al-Asad ne, ya nuna cewa Al-Aswad hakika kakanta ne. Don haka dan uwansa Abu Salama ya kasance kakanta.
Mahaifiyar Fatima ita ce Fatima bint Abd al-Uzza bn Abi Qays daga zuriyar Amir bn Luayy. Fatima tana da ‘yan’uwa biyu Habbar da Abdullah, wadanda suka musulunta da wuri.
A watan Maris 624 Al-Aswad bn Abd al-Asad ya yi yaki a bangaren kafi**ran Makka a yakin Badar. A yakin ne kawun Annabi Muhammad (SAWW) Hamza (AS) ya kashe shi.
Fatima ta musulunta kuma ta yi mubaya’a ga Annabi Muhammadu (SAWW). Ba a bayyana ko ta yi haka ne a lokacin da aka ci Makka ko a daga baya ba.
Laifin Sata
Kwanan wata da lokacin da Fatima ta aikata laifin, an yi sabani. Ya kasance ko dai a lokacin Yakin Makka a watan Janairu 630 ko kuma lokacin Hajjin bankwana a watan Maris 632.
A cewar Uwar muminai Sayyada A’isha (RA), ta kasance tana aron kaya sannan ta musanta cewa ta karba. Yana daga cikin al’adarta satar “kayan ado”. Wata rana ta fita da daddare, sai ta shiga wani sansanin matafiya, ta sace musu jakunkuna guda biyu, sai dai tayi rashi sa’a an kama ta, sai matafiya suka kama ta suka daure ta.
Hukunci
Da safe aka kai ta gaban Annabi Muhammad (SAWW). Annabi ya hukunta a yanke hannunta (kamar yadda Allah yace a cikin Alkur’ani mai girma). {Barawo da ɓarauniya to ku yanke hannayensu} [al-Ma’ida: 38].
Kuraishawa sun tausaya mata sosai, kuma suka nemi aji tausayin ta a rage mata hukunci. Fiye da mutum ɗaya ne suka yi mata roƙo wajen Annabi Muhammad (SAWW). Yan uwan Fatima su na ganin cewa, wanda kawai zai iya fuskantar Annabi Muhammad (SAWW) don nema mata afuwa, kuma wanda zai iya yin tasiri a kansa, shi ne, Usama ibn Zaid (RA), saboda Manzon Allah (SAWW) yana jin maganarsa. Yan uwan na ta sun yi magana da Usama, wanda shi kuma ya je wajen Annabi (SAWW).
Usama ya yi magana a madadin Fatima, nan da nan fuskar Annabi Muhammad (SAWW) ta canza cikin tsananin fushi, sai ya tambaye shi: “Shin kana yin cẽto ne don ka karya ɗaya daga cikin dokokin Allah ? Sai Usamatu ya ce: “Ya Manzon Allah ka nema mini gafara!”
Sai Fatima ta nemi mafaka wajen Ummu Salama (RA), wacce ta kasance daya daga cikin iyayen mummunai (matar Annabi SAWW). Amma Annabi ya umurci matarsa da ta kyale ta, yana mai cewa ba zai bar hukuncin ba ko da diyarsa ce ta aikata.
Da Magariba Annabi (SAW) ya miƙe ya yi wa mutane wa’azi. Sai ya yi godiya ga Allah, sannan ya ci gaba da cewa: “Ya ku al’ummai, al’ummomin da suka gabace ku sun bace, wasu kuma an halaka su, domin idan mai girma ya yi sata, sun kasance suna yi masa afuwa, amma idan wani mai rauni a cikinsu ya yi sata, sai su zartar masa da hukunci. Na rantse da wanda rayuwata ke hannunsa, ko da Fatima bint Muhammad ce, ta yi sata zan yanke hannunta.
Bayan wannan sanarwar, ya ba da umarnin a zartar da hukuncin. ya koyar da cewa: “A yanke hannu duk wanda ya saci wani abu da ya kai darajar rubu’in dinari ko fiye. Sai a ka yanke hannunta, “ta fita da hannunta na digon jini.
Tuba
Uwar muminai sayyada Aisha (RA) ta tabbatar da cewa Fatima “ta tuba da gaske”. Lokacin da take da bukata takan ziyarci Sayyida Aisha (RA), wacce ta dinga mika bukatarta ga Manzon Allah (SAWW).
Fatima tayi aure a lokacin Annabi Muhammad (SAWW) yana raye, Alkunyarta ita ce Umm Amr, wannan ya nuna cewa tana da ɗa mai suna Amr.
Madogarar Wannan Rubutu
1. Sahih Muslim; 17:4190.
2.Sahih Bukhari; 4:55:2505.
3. Muhammad ibn Saad, Tabaqat vol. 8. Translated by Bewley, A. (1995). The Women of Madina, p. 185. London: Ta-Ha Publishers.
4. Muhammad ibn Ishaq, Sirat Rasulallah. Translated by Guillaume, A. (1955). The Life of Muhammad, p. 311. Oxford: Oxford University Press.
5. Muhammad ibn Ishaq, Sirat Rasulallah. Translated by Guillaume, A. (1955). The Life of Muhammad, p. 329. Oxford: Oxford University Press.
6. Muhammad ibn Ishaq, Sirat Rasulallah. Translated by Guillaume, A. (1955). The Life of Muhammad, p. 528. Oxford: Oxford University Press.
7. Muhammad ibn Ishaq, Sirat Rasulallah. Translated by Guillaume, A. (1955). The Life of Muhammad, p. 299. Oxford: Oxford University Press.
8. Muhammad ibn Saad, Tabaqat vol. 8. Translated by Bewley, A. (1995). The Women of Madina, p. 184. London: Ta-Ha Publishers.
9. Muslim 17:4188
10. Muslim 17:4189.
11. Bukhari 8:81:779.
12. Muslim 17:4187.
13. Bukhari 8:81:780.
14. Muhammad ibn Saad, Tabaqat vol. 3. Translated by Bewley, A. (2013). The Companions of Badr, p. 470. London: Ta-Ha Publishers.
Fassarar Muhammad Cisse ✍️.
Leave a Reply