Hanyoyi 10 da Za Su Sa Allah Ya So Ka – Yadda Ake Samun Soyayyar Allah

Hanyoyi 10 da Za Su Sa Allah Ya So Ka – Yadda Ake Samun Soyayyar Allah
Facebook
Hanyoyi 10 da Za Su Sa Allah Ya So Ka – Yadda Ake Samun Soyayyar Allah
Facebook

 

Hanyoyi 10 da Za Su Sa Allah Ya So Ka – Yadda Ake Samun Soyayyar Allah

 

SABUBA GUDA GOMA (10) DA SUKE SA ALLAH YA SO BAWANSA

 

Alal hakika soyayyar Allah da yardarsa ga bawa su ne kololuwar burin bawa a rayuwarsa ta duniya da lahira.

Dalilin da yasa nace Allah ya tsine wa Baban Mu

Al- Allama Ibnul Qayyim (r) ya ce:

الأسباب الجالبة للمحبة، والموجبة لها وهي عشرة.

أحدها: قراءة القرآن بالتدبر والتفهم لمعانيه وما أريد به، كتدبر الكتاب الذي يحفظه العبد ويشرحه. ليتفهم مراد صاحبه منه.

الثاني: التقرب إلى الله بالنوافل بعد الفرائض. فإنها توصله إلى درجة المحبوبية بعد المحبة.

الثالث: دوام ذكره على كل حال: باللسان والقلب، والعمل والحال. فنصيبه من المحبة على قدر نصيبه من هذا الذكر.

الرابع: إيثار محابه على محابك عند غلبات الهوى، والتسنم إلى محابه، وإن صعب المرتقى.

الخامس: مطالعة القلب لأسمائه وصفاته، ومشاهدتها ومعرفتها. وتقلبه في رياض هذه المعرفة وميادينها. فمن عرف الله بأسمائه وصفاته وأفعاله: أحبه لا محالة. ولهذا كانت المعطلة والفرعونية والجهمية قطاع الطريق على القلوب بينها وبين الوصول إلى المحبوب.

السادس: مشاهدة بره وإحسانه وآلائه، ونعمه الباطنة والظاهرة. فإنها داعية إلى محبته.

السابع: وهو من أعجبها، انكسار القلب بكليته بين يدي الله تعالى. وليس في التعبير عن هذا المعنى غير الأسماء والعبارات.

الثامن: الخلوة به وقت النزول الإلهي، لمناجاته وتلاوة كلامه، والوقوف بالقلب والتأدب بأدب العبودية بين يديه. ثم ختم ذلك بالاستغفار والتوبة.

التاسع: مجالسة المحبين الصادقين، والتقاط أطايب ثمرات كلامهم كما ينتقي أطايب الثمر. ولا تتكلم إلا إذا ترجحت مصلحة الكلام، وعلمت أن فيه مزيدا لحالك، ومنفعة لغيرك.

العاشر: مباعدة كل سبب يحول بين القلب وبين الله عز وجل.

مدارج السالكين (3/ 18 – 19)

Dalilin da Ya Sa Sufaye Suke Ƙaryata Hadisan Manzon Allah – Bayani da Hujoji

“Sabuba da suke janyo ma bawa soyayyar Allah, kuma suke samar da ita su goma ne:

 

1- Karanta Qur’ani da Tadabburi (lura da ma’anonin abin da ake karantawa) da fahimtar ma’anoninsa da abin da ake nufi a cikinsa, kamar lura da littafin da bawa yake haddacewa yake sharhinsa don ya nemi fahimtar manufar marubucinsa.

2- Neman kusaci zuwa ga Allah da nafilfili bayan farillai, saboda za su isar da shi ga darajar zamowa abin so bayan ta soyayya. (Sai bawa ya so Allah kafin ya zama abin so a wajen Allah).

3- Dawwama a kan zikirin Allah a kowane hali; da baki, da zuciya, da aiki da hali (yanayi), kaso da bawa zai samu na soyayyar Allah shi ne gorgodon kasonsa a wannan zikiri.

4- Fifita abubuwan da Allah yake so a lokacin da son zuciya yake rinjayar mutum, da firin ciki zuwa ga ababen da yake so ko da kuwa isa garesu zai wahalar.

5- Zuciya ta rinka leka sunayensa da siffofinsa, da halartosu da neman saninsu, da jujjuyawarsa a dausayin wannan ilimi da fagagensa. Saboda DUK WANDA YA SAN ALLAH DA SUNAYENSA DA SIFOFINSA DA AIYUKANSA TO BABU MAKAWA ZAI SO ALLAN. Saboda haka ne “Mu’attila” (masu kore Siffofin Allah) da mabiya tafarkin Fir’auna (masu musun samuwar Allah), da Jahamiyya suka kasance masu yanke hanya wa zukata tsakaninsu da isa zuwa ga Allah abin soyayya.

6- Halarto alheransa ga bayi da kyautansa da ni’imominsa, da ni’ima ta bayyane da ta boye, lallai hakan yana janyo sayayyarsa.

7- Karayar zuciya gaba dayanta a gaban Allah Madaukaki, wannan shi ne mafi ban sha’awa a cikinsu, babu abin da zai iya bayyana wannan sai dai kawai sunaye da jumloli.

8- Kebancewa da Allah a lokacin saukowansa daga sama (a daya bisa ukun dare na karshe) don ganawa da shi da karanta Maganarsa (Qur’ani), da tsayuwa da zuciya, da siffantuwa da laduban bauta a gabansa, sa’annan ya cikata da Istigfari (neman gafara) da tuba.

9- Zama da masoya Allah masu gaskiya, da tsintar kyawawan maganganunsu kamar yadda ake zaben dad’ad’an ‘ya’yan itatuwa. Kar ka yi Magana sai in maslahar maganar ta zama mai rinjaye, kuma ka san cewa akwai karuwa a halinka, kuma zai amfanar da waninka.

10- Nisantar dukkan wani sababi (na Shirka ko Bidi’a ko Zalunci ko Fasikanci ko Sabo ko Gafala) da zai shiga tsakanin zuciya da Allah ya rabasu”.

 

Dan uwa ga nan fa aiki a gabanmu!

 

Allah ya sa mu dace da samun soyayyar Allah Ubangijinmu.


Published on: March 16, 2025. at: 10:32 pm

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*