Hanyoyi 5 na kare kai daga kamuwa da ciwon ƙoda

Hanyoyi 5 na kare kai daga kamuwa da ciwon ƙoda
Shan Ruwa da Yadda Yake Taimakawa Kodar Jiki
Hanyoyi 5 na kare kai daga kamuwa da ciwon ƙoda
Shan Ruwa da Yadda Yake Taimakawa Kodar Jiki

 

Hanyoyi 5 na kare kai daga kamuwa da ciwon ƙoda

 

Ciwon koda, ciwo ne da ke barazana ga lafiyar al’umma a duniya, kuma saboda girmansa ya sa majalisar ɗinkin duniya ta ware rana domin tunawa da cutar koda ta duniya.

 

Alkalumma sun nuna cikin mutum 10 a duniya daya daga cikinsu za a same shi da ciwon koda wanda ya nuna girman barazanar ciwon a duniya.

 

An kebe ranar domin fadakar da al’umma da yunkurin rage yawan masu kamuwa da cutar da sauran dangoginta a fadin duniya.

 

A kan tuna da ranar ce duk Alhamis ta biyu na watan Maris.

 

A Najeriya wani rahoton kungiyar masu kula da lalurar koda ya ce ‘yan kasar miliyan ashirin da biyar ne ke fama da ciwon, abin da kan sa kodar ba ta aiki yadda ya kamata har sai an rika zuwa wanki.

 

Kididdigar da kungiyar ta fitar ya nuna cewa akasarin masu fama da cutar matasa ne.

 

Alamomin ciwon koda kamar yadda likitoci suka bayyana sun hada da kumburi da yawan kasala da fitsari mai kumfa da yawan amai har zuwa jijjiga.

 

8 Maris 2025

Dr Abdurrashid Sarki Iliyasu ƙwararren likitan koda a asibitin kasa da ke Abuja, ya yi bayani kan hanyoyin kare kai daga kamuwa da ciwon koda

 

Ya ce kariya daga kamuwa da ciwon ba wani abu ba ne mai wahala ko tsada domin ba abubuwa ne masu girma ba da za a ce ba za a iya yi ba.

 

Ya ce mutane za su iya kare kansu daga kamuwa da cutar koda ta hanyar cin abinci mai gina jiki da kuma kiyaye duk abubuwan da aka ce suna janyo cutar.

 

Amma duk wanda ya samu ciwon koda zai sha wahala ta tsadar magunguna da sauran matakai na waraka. Matakan kariya sun hada da:

 

Kaucewa shan magunguna

Ana son mutum ya kiyaye magungun da yake sha, ya kare kansa da shan magungunan da ba a san sahihancinsu ba, da suka shafi na gargajiya da shan na Bature da ya wuce kima.

 

Likita ya ce shan wasu magunguna na bature fiye da kima na haifar da ciwon koda.

 

Sannan ya ce ya kamata duk maganin da mutum zai sha ya kasance ya nemi shawarar likita domin kiyaye lafiyar koda.

 

Zuwa asibiti a kai a kai

Duk lokacin da mutum ya samu rashin lafiya ko da zazabi ne, ya kamata ya yi kokarin zuwa asibiti domin tabbatar da ya samu kulawar da ta dace ta kwararrun likita don samun maganin da ba zai taba masa koda ba.

INTELREGION

Likita ya ce hawan jini da ciwon suga na cikin cututtukan da ke haddasa ciwon koda – ya kamata mutum ya dinga kokarin zuwa asibiti don a ba shi magungunan da suka dace da kuma kula da ciwonsa na hawan jini ko ciwon sugari don kare shi daga kamuwa da ciwon koda.

 

Zuwa asibiti, a cewar liktita zai taimaka duba duk wasu abubuwa da za su kawo ciwon koda domin a magance su da wuri ba tare da an kai yanayin da kodar ta mutu gaba daya ba ta aiki a jiki ba.

Dalilin da Ya Sa Sufaye Suke Ƙaryata Hadisan Manzon Allah – Bayani da Hujoji

Yawaita shan ruwa

Ana son mutum ya yawaita shan ruwa, likitoci na bada shawarar shan ruwa akalla gora uku wato lita uku a rana daga safe zuwa washegari.

 

Rashin shan isasshen ruwa a lokacin gumi kan janyo ciwon koda.

 

Yawan shan ruwa zai sa mutum ya samu isasshen ruwa a jikinsa kuma jini yana zuwa kodarsa don ta yi aiki sosai.

 

Rage shan gishiri da yawa

Cin gishiri da yawa yana cikin abubuwan da ke janyo hawan jini, likitoci na bada shawarar rage yawan cin gishi domin idan ya yi yawa a jiki yakan taba koda.

 

Motsa jiki

Motsa jiki hanya ce ta waraka daga cuttuka da za su kare koda.

Yadda Ake Samun Followers Cikin Kankanin Lokaci a Social Media – Hanyoyi Masu Sauƙi da Inganci

Likita ya bada shawarar a dinga motsa jiki domin zai taimakawa wajen magance hawan jini da ciwon suga tare da kare koda.


Published on: March 13, 2025. at: 7:19 pm

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*