Liverpool ba ta da niyyar sayar da Salah, Rashford na cikin rashin tabbas

 

152db6f0 06a6 11ef b9d8 4f52aebe147d

Liverpool na fatan Mohamed Salah ya cigaba da zama da ita a wannan kaka, inda take fatan ya cigaba da kasancewa cikin tawagarta a sabuwar kaka. (The Athletic – subscription required)

Daraktan wasannin Liverpool zai jagoranci tattaunawar sabunta kwantiragin Salah mai shekara 31, wanda yarjejeniyar da yake kai yanzu sai 2025 za ta kare. (Times – subscription required)

Marcus Rashford na cikin rashin tabbas kan ko ya bar Manchester United, adaidai lokacin da Paris St-Germain ke nuna ɗan kwadayinta kan ɗan wasan mai shekara 26. (i)

Ɗan wasan Crystal Palace mai shekara 23, Marc Guehi, ya kasance wanda Liverpool ke farauta domin maye gurbin ɗan wasanta na Kamaru Joel Matip mai shekara 32 da ke shirin barin kungiyar. (Football Insider)

Ajax ta shirya sake dauko Erik ten Hag da zaran Manchester United ta kore shi a wannan kaka. (Mail)

West Ham ta sake farfado da kaunar da take yi wa kocin Sifaniya, Julen Lopetegui bayan samun labarin cewa AC Milan na nazarin ko ta dauko shi domin maye gurbin kocinta Stefano Pioli. (Guardian)

Kungiyar ta kuma zaku ta saye ɗan wasannan mai shekara 25 daga Coventry Callum O’Hare da mai taka leda a Hull Jacob Graves mai shekara 23 a wannan kaka. (Guardian)

Mai rike da kofin gasar Championship ta Ingila Leicester za ta samu damar sayen ‘yan wasa a kasuwar cinikin ‘yan wasanni ta bana duk da takunkumi da take fuskanta daga hukumar wasannin Ingila. (Mail)

Sai dai kuma, dole ta sayar da ‘yan wasanninta kafin 30 ga watan Yuni domin cimma kaidojin cinikin ‘yan wasa. Yanzu haka ɗan wasanta na tsakiya mai shekara 25 Kiernan Dewsbury-Hall ya ja hankalin Brentford da Brighton da kuma Fulham. (Mail)

Manchester United na shirin nada Dan Ashworth a matsayin daraktan wasanni a wannan kaka a kokarin cimma yarjejeniya da Newcastle a wannan kaka. (Football Insider)

Tsohon ɗan wasan Ingila Jermain Defoe mai shekara 41, na iyasamun aikinsa na farko na horarwa idan aka yi narasa ya daidaita da Sunderland. (Sun)


Published on: April 30, 2024. at: 5:45 am

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*