KADAN DAGA LITTAFIN MAZAN JIYA Lokacin da sharlis tagama zancen zuci sai kawai ta juya ta fice daga turakar sarki laffaru ta nufi inda bargar dawakai yake da zuwa saita shige bargar dawakan ta kamo wani farin ingarman doki ta fito dashi koda bawan dake kulada dawakan ya hango sharlis tafito da doki saiya ruga da gudu ya daukowa sharlis siddi ya daura mata cikin hanzari sharlis ta daka tsalle ta haye kan dokin tana goye da danta shaddad sannan ta zaburi dokin ta fice daga gidan sarautar gabadaya ta nufi kofar gari kai tsaye. A wannan lokacin ne sarki laffaru ya fito daga turakar sa ya iso babban harabar gidan sarautar inda ya iski dakarun kasar na yaki kimanin mutum dubu dari uku da hamsin sunata shirye-shiryen fita wannan yaki sai fito da makamai sukeyi masu daurawa dawakai siddi nayi masu tanadar guzuri nayi hakama masu gyaran baka da kifiyoyi koda ganin haka sai sarki laffaru ya daka musu tsawa yace ayi sauri a kammala shiri domin gacan abokan gaba har sun iso kusada kofar gari kodajin wannan batu sai gabadaya dakarun suka cika da mamakin yadda akayi sarki yasan abokan gaba sun iso kusada kofar gari alhali yana can cikin gidan sarauta kuma daga can nesa aka jiyo tambarin yakin na abokan gabar aikuwa take saiga sarkin kofa ya rugo da gudu a firgice da zuwan sa saiya zube kasa a gaban sarki laffaru yace ya shugabana ga abokan gaba nan sun iso kofar gari kuma babu kowa a waje face matar ka sharlis ita kadai akan doki ta fuskance su kodajin wannan batu sai sarki laffaru yace ai maza akawo masa doki nan dannan kuwa aka kawo dokin ya hau ya zabure shi da gudu yayi waje aikuwa sai dakarun gabadaya suka bishi a baya kamar tururuwa da iyalanta sun fito daga rami. A can kofar gari kuwa lokacin da dakarun sarki nurbas suka iso kusada kofar birnin kufa sarki nurbas ne a gaba sai yaja linzamin dokin sa ya tsaya lokaci guda gabaki daya miliyoyin dakarun nasa wanda adadin su yakai miliyan uku sai suka tsaitsaya sarki nurbas ya waiga baya ya dubi wadannan dakaru nasa yaga yawansu sai yaji wani irin dadi a ransa domin yasan a yau dai koh sama da kasa zata hade saiya murkushe birnin kufa ya kama sarki laffaru yayi masa kisan gilla sannan ya kwashe duk dukiyar sa sannan ya daura wakilin sa akan karagar mulkin gama aiyana hakan keda wuya acikin zuciyar saiya waigo ya dubi kofar birnin kufa domin ya bada umarni a afkawa garin a fasa kofa da karfin tsiya a shiga ya waigowa haka sai yaga wata jaruma jal daya bisa kan doki sanye da farin sulke ta rufe fuska kuma ta zare takobi tana kallon su alamarin dayayi matukar bawa sarki nurbas mamaki kenan kawai saiya bushe da mahaukaciyar dariya ya juya ya dubi dakarun sa yace hakika sarki laffaru ya haukace inbanda wanda yasamu tabin kwakwalwa waye zai tura jaruma guda daya jal tazo ta yaki wannan runduna tamu koda gama fadin haka sai sarki nurbas yasake bushewa da dariya ya dubi zakakuran mayakan sa guda uku wadanda ya yarda da jarumtakar su yace maza kuje ku kama waccar jarumar kuyi mata tsirara sannan kujata a kasa bayan kun daure hannayen ta da igiya ku kawota nan gabana tana mai wulakanta kodajin wannan batu sai wadanan dakaru guda uku suka zaburi dawakansu suka nufi kofar birnin kufa inda sharlis ke tsaye adaidai wannan lokacin ne sarki laffaru da dakarun sa suka fito daga cikin birnin koda sharlis tagansu sai ta daga musu hannu tana mai yi musu nuni da kada su kariso inda take nan take kuwa sarki laffaru yaja tunga suma duka dakarun nasa sukayi koyi dashi yayin da sharlis taga wadan nan dakaru na sarki nurbas sun durfafota a sukwane bisa dawakai saita mayar da takobin ta cikin kufe sannan ta zabure dokin ta a guje domin ta tare su tun kafin suzo su risketa lokacin dabai wuce taku biyar ba su hadu itada dakarun uku saita daka tsalle daga kan dokin nata tayi sama kamar tsuntsuwa tasa kafarta ta gabza musu naushi a fuskokin su duk su ukun suka tuntsuro daga kan dawakan su suka zube a kasa ita kuwa akan dokin ta ta diro ta zauna dirshan koda ganin wannan bajinta da sharlis tayi sai gabadaya dakarun sarki laffaru suka fara tafka radadi cikin tsanin fishi dakarun uku suka mike tsaye zumbur cikin fishi suka zare takobbu nan su suka ruga gareta cikin kunar rai da mugun nufi domin su huce kunyar data basu da isowar su sai daya daga cikin su ya sokawa dokin ta takobi a ciki take dokin ya durkushe kasa zai kayar da ita amma sai tayi sama taci gabada gabzar dakarun da kafarta sukuwa sukayita kaimata sara tana gocewa suna samun iska nan fa duk jama'ar dake filin yakin suka cikada matukar al'ajabi da irin wannan jarumtaka na sharlis domin saidata shafe dakika dari uku da sittin kafarta bata taba kasa ba tanayiwa wadan nan dakaru luguden duka da kafafun ta har katantanwa take a sama ta juya gabas da yamma kudu da arewa cikin zafin nama har tsawon wannan lokacin dayansu bai samu taba jikin taba da takobin sa kuma dukta farfasa musu baki da hanci jini na zuba yayin da duka yakai duka sai gabadayan su suka galabaita suka zube kasa magashiyan a sannan ne ta diro gaban su tayi nuni da hanun ta na hagu agare su saiga rigunan su da wandu nan su yazamana cewa kowanne acikin su babu komai a jikin sa sai dan kamfai nan fa dakarun uku suka kamu da tsananin kunya suka manne da junansu suna boye fuskokin su al'amarin dayasa sarki laffaru da dakarun sa suka bushe da dariya kenan nan take sharlis ta jefa wata igiya izuwa ga dakarun su uku ta sarkalo wuyan su tare sannan tayi tsalle ta sake hawa dokin ta tana rike da wannan igiya taja dakarun nan a kasa ta durfafi inda abokan gaba suke a wannan lokaci ne zuciyar sarki nurbas tafara tafarfasa kamar zata kone sbd fusata. comments and likes
Leave a Reply