

Soyayyar Annabi (SAW): Maulidi Da Wakoki Bidi’a Ne Ko Sunnah?
SOYAYYAR ANNABI (SAW)
Ba’a gane soyayyar Annabi da taron maulidi, domin Annabi bai koyar ba
Ba’a gane soyayyar Annabi da wakokin bege domin Annabi bai koyar ba
Ba’a gane soyayyar Annabi da kida da waka, wannan dabi’ace ta masu bin addinin nasara
Ana gane son Annabi ne kadai ta hanyar yin abinda yace ayi, da barin aikata abinda ya hana
Idan ka karbi wayar cikakken dan darikar sufaye ka duba babu abinda zaka samu a ciki sai wakokin begen Annabi hade da kida da wakoki masu dauke da kalaman shirka da wuce gona da iri
Idan kuma ka karbi wayar Ahlussunnah na gaskiya ka duba ba abinda zaka samu sai Karatun Qur’ani da Hadisi da wa’azozin Malamai masu shiryarwa zuwa ga hanyar tsira
Shin Takalmin Annabi Muhammad (S.A.W) Yafi Komai Daraja? Gaskiyar Bayani a Musulunci
Annabi bai koyar da kida da wakokin begensa ba wanda yau aka dauka a matsayin addini, Annabi Qur’ani da Hadisai ya koyar, shiyasa mu Ahlussunnah muka dukufa akan Qur’ani da Hadisi
Don haka idan aka duba Wallahi mu Ahlussunnah mun fi ‘yan darikun sufaye Kaunar Annabi (SAW) da bin karantarwansa tsantsa
Musulunci bai bar komai ba sai da yayi bayani a kai, kuma addinin Musulunci ya cika baya bukatan kari
Don haka tashi ayi karatu a dena wuce gona da iri, imba haka ba kamar yadda Annabi Isah zai yi baram-baram da wadanda suke cewa su masoyansa ne haka ‘yan darikun sufaye masu wuce gona da iri zasuyi da Annabi (SAW) a ranar Hisabi
Yaa Allah Ka dauki rayukanmu a wannan tafarki na Sunnah muna masu bin karantarwan Annabi da magabatan kwarai
Leave a Reply