

Yadda Ake Samun Followers Cikin Kankanin Lokaci a Social Media – Hanyoyi Masu Sauƙi da Inganci
Mai neman followers ido rufe.
Na ba ka shawara?
Ba abin da zai ja maka followers shafinka kamar abin da kake wallafawa. Mutane za su bibiye ka ne, ba don kai kai ne ba, sai don VALUE da za ka iya samarwa da zai amfane su a rayuwa.
Valued contents sai iya kasance na ilimi ne, ko nishaɗi, wayar da kai, koyar da sabbin dabarun rayuwa ko amfani da sabuwar fasahar, nuna rayuwar da za su yi sha’awa… abu dai zai amfani mutane ta addini, ko tattali, ko lafiya, ko zamantakewa…
Ai kamar a duniyar zahiri ne, mutane na raɓar abin da za su mora ne. Duba attajirai da masu madafun iko (mulki), da zarar ba wani value da zai ƙara a rayuwar mutane, za su sake shi su kama wani. Haka ma social media ta ke.
Mene ne hadafinka na tara followers Monetization? Monetization ma sai kana samar da value, organic followers suna tara maka engagements.
Social media marketing? Copywrite, visual identity, da sauran strategies ne zai ja hankali mutane zuwa ga shafinka.
Mutane za su je shafinka, idan sun ga babu dalilin da zai sa su bibiye ka, za su yi REVERSE. Duk waɗanda ka ga sun tara followers (idan followers kake sha’awa), ba roƙa suka yi, value nasu ya jawo musu. Kai kuma me za ka samar? Ba ma buƙatar riƙon kowa ya yi following naka, ka samar da value.
#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #AliMotives
Leave a Reply