APC, EFCC na shirin gurguntar da jihohin PDP – Secondus

– Shugaban jam’iyyar PDP, Prince Uche Secondus, yayi zargin cewa hukumar EFCC da rundunar yan sanda sun shiga wani yarjejeniyar sirri da jam’iyyar APC don gurguntar da jihohin PDP
– Secondus ya kara da cewa suna yunkurin ne domin dakatar da kudirin PDP na yin tazarce da ceto kasar daga mugun mulkin APC
– Jam’iyyar APC ta yi watsi da zargin cewa jam’iyyar PDP na fadin karya ne
Shugaban jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Prince Uche Secondus, a ranar Laraba, 12 ga watan Disamba yayi zargin cewa hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) da rundunar yan sanda sun shiga wani yarjejeniyar sirri da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) don gurguntar da jihohin PDP.
Secondus ya kara da cewa suna yunkurin ne domin dakatar da kudirin PDP na yin tazarce da ceto kasar daga mugun mulkin APC.

Sai dai, jam’iyyar APC ta yi watsi da zargin cewa jam’iyyar PDP na fadin karya ne.
Secondus a wata sanarwa daga hadiminsa, Mista Ike Abonyi, yayi ikirarin cewa PDP na sane da duk wani shiri na APC don tabbatar da cewar jihohin PDP sun tagayyara ta yadda ba za su iya mayar da hankali wajen neman tazarcensu ba.

Shugaban PDP din yayi zargin cewa sake tura wasu kwamishinoni jihohin Bayelsa, Akwa Ibom da Ebonyi duk kokari ne na hana jam’iyyarsa yin tazarce a jihohin guda uku.
Sai dai babban sakataren labarai na APC, Mista Lanre Issa-Onilu yace yan Najeriya su share PDP domin ba gaskiya take fadi ba.


Published on: December 13, 2018. at: 2:24 pm

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*