Rundunar ‘yan sandan Najeriya, reshen jihar Katsina, ta sanar da samun nasarar damke wata tawagar ‘yan fashi da makami ta mutane biyar da suka dade suna addabar garuruwan Jihar Katsina da kewaye.
Jam’ian rundunar ‘yan sandan sun yi nasarar cafke ‘yan fashin ne a jiya, Juma’a, bayan aikata wani fashi a garin Funtuwa.
Isa Gambo, kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar Katsina, ya bayyana cewar alhaki ne ya kama ‘yan fashin bayan sun aikata fashi a gidan wani mutum mai suna Haruna Idris dake unguwar Dan-Dutse a garin Funtuwa.
Gambo ya lissafa sunayen ‘yan fashin kamar haka: Umar Yahaya (shekaru 24), Abdulmalik Yahaya (shekaru 20), Abdulrashid Musa (shekaru 20), Abdurrahaman Suleiman da (shekaru 21), dukkansu mazauna kauyen Maigamji dake karkashin karamar hukumar Funtuwa.
Ya kara da cewar an yi nasarar samun makamai da suka hada da bindiga, bindigar wasan yara daya, wukake masu kaifi guda biyu, adda, cocilan, dubu tara da naira tamanin, da wayoyin hannu 4, da kuma hular soji guda daya.
Kazalika rundunar ‘yan sandan ta sanar da kama mutane 12 da ake zargi da satar mutane da satar shanu a garuruwan Dandume da Safana.
An kama su ne yayin da suka kai farmaki kauyen Dallawa Mahuta inda suka kashe wani matashi mai suna Aminu Maharazu, mai shekaru 20.
Sun shiga hannu ne bayan artabu da jami’an ‘yan sanda. Mutanen kauyen sun kashe uku daga cikin ‘yan fashin kafin karasowar jami’an ‘yan sanda, ragowar kuma sun guda zuwa cikin daji.
An baza jam’ian ‘yan sanda zuwa cikin jejin domin kama ragowar da suka gudu.
An gano gawar Isiya Bello, dan asalin karamar hukumar Sabuwa, kasurgumin mai garkuwa da mutane da ya addabi garuruwan Dandume, Sabuwa, da Ankara, daga cikin ‘yan ta’addar da mutanen kauyen suka kashe.
Leave a Reply