Kwana 200 ba Zidane a Madrid, ko da canji?

A ranar 31 ga watan Mayun 2018, Zinedine Zidane cikin bazata ya ajiye aikin horar da Real Madrid, bayan da ya lashe kofin Zakarun Turai uku a shekara biyu da rabi da ya yi a Santiago Bernabeu.
Kawo yanzu ya cika kwana 200 da ya bar kungiyar, tun daga nan ne Madrid ta dunga sauya masu horar wa, sannan wasu fitattun ‘yan wasanta suka sauya kungiya.
Real na fama da kalubale wanda daya ne daga cikin da ta fuskanta mafi muni a rashin kokari a fagen tamaula, abin tambaya shi ne me ya sauya tun barin Zinadine Zidane ne?
Real Madrid ta sanar da nada Julen Lopetegui a matsayin wanda ya maye gurbin Zidane, hakan ya sa kungiyar cikin rikici da hukumar kwallon Spaniya, bayan kocin na da yarjejeniyar horar da Spaniya a kofin duniya, dalilin haka ya hakura da gasar kofin duniya.
Daga nan ne Cristiano Ronaldo ya koma Juventus a ranar 10 ga watan Yuli, hakan ne ya sa Real ta yi ban kwana da dan wasan da ke ci mata kwallo 50 a kaka guda.
Bayan da Zidane da Cristiano Ronaldo suka bar Bernabeu ne Atletico Madrid ta lashe European Super Cup, bayan da ta yi nasara a kan Real, kuma karo na biyu a wasan hamayya.
Madrid ta yi wasa dakika 481 ba tare da ta ci kwallo ba a karkashin koci Lopetegui, kuma daya daga tarihi mafi muni da kungiyar ta yi.
Bayan da Barcelona ta doke Real Madrid da ci 5-1 a Camp Nou ne aka kori Lopetegui a ranar 29 ga watan Oktoba, aka bai wa Santiago Solari kocin rikon kwarya.
Solari ya ci wasa tara da rashin nasara a biyu daga 11 da ya ja ragama, kuma a ranar Laraba Madrid za ta buga gasar cin kofin Zakarun nahiyoyin duniya a Abu Dhabi.
Haka kuma kungiyar ta kai matakin kungiyoyi 16 da suka kai zagayen gaba a gasar Zakarun Turai ta Champions League, tana kuma cikin wadanda ke buga Copa del Rey.
Watakila Real Madrid ta dauki wani kofin kafin bikin Kirsimeti.


Published on: December 19, 2018. at: 3:46 pm

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*