Kwastam fa ta tara wa gwamnati kudin da bata taba gani a lalitarta ba daga hukuma daya

– Hukumar kwastam ta kasa ta samu kudin shiga har Naira tiriliyan 1.1
– Hukumar ta kwace kayan fasa kwabri har na Naira biliyan 40 tsakanin watan Janairu zuwa Nuwamba
-“Kudin da aka samu a shekarar nan yafi na shekarar da ta gabata da Naira tiriliyan 1.03″inji Mista Attah

Hukumar kwastam ta kasa a ranar Alhamis tace ta samu Naira tiriliyan 1.1 a matsayin kudin shiga kuma ta kwace kayan fasa kwabri na kudi kimanin Naira biliyan 40 tsakanin watan Janairu zuwa Nuwamba na wannan shekarar.
Jami’in hulda da jama’a na hukumar, mataimakin kontrola, Joseph Attah, ya bayyana hakan ga manema labarai a Abuja.
Mista Attah yace kudin da aka samu ya zarce na shekarar da ta gabata da Naira tiriliyan 1.03.
Mai magana da yawun hukumar ya sanar da ofishin dillancin labarai cewa kwantena 59 ta tramadol da wasu kwayoyin suka kwace a wannan lokacin.
Yace kwantena 40 aka kwace a filin jirgin ruwa na Apapa, 10 a Tincan sai 9 a Onne dake fatakwal jihar Rivers.
Mista Attah yace duba da irin kwace kayayyakin da sukayi, wannan na nuna cewa hukumar ta kokarta wurin toshe hanyoyi tare da tabbatar da tsauraran dokokin sumogal a wannan shekarar.
Kamar yadda yace, raba jami’an su yanda ya kamata shima ya taka rawar gani wurin tabbatar da tsaron.

“Munsan cewa maida hankali da mukayi, kamawa da gurfanar da masu sumogal ya sabawa ra’ayin wasu mutanen. Da wannan nasarorin, yana nuna mun tsaya da kafafun mu kuma shiyasa wasu makiya suke shiga gari suna yada cewa mun hana kasuwanci kuma muna assasa rashawa.”
“Jami’an mu sunki karbar cin hancin Naira miliyan 150 wanda wadanda ake zargi suka basu don kubutar da kasar nan daga amfani da miyagun kwayoyi. Hukumar kwastam karkashin shugabancin Col. Hameed Ali bazata yaudaru ba gurin tsayuwar tsayin daka da tayi don kawo karshen makiyan kasa. Muna kara jaddada cewa duk wasu masu cinikayya tsakanin su da kasashen ketare da su bi dokoki sau da kafa.” inji shi


Published on: December 7, 2018. at: 9:14 pm

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*