Lambar Najeriya ta fito a cikin Kasashen da ‘Yan ta’adda ke barna

Mun samu labari daga Jaridar nan ta Premium Times cewa an fitar da jerin Kasashen da su ka fi kowane fama da masifar ta’addanci a Duniya, a wannan shekarar ma dai Najeriya ta zo cikin sahun farko.

A wannan shekara ma, Najeriya ta zo ta 3 a kaf Duniya a cikin jeringiyar Kasashen da ke fuskantar hare-haren ‘Yan ta’adda. A 2014 dai Najeriya tazo 4 a Duniya, sai dai tun bayan nan ne kasar ta makale a matsayin ta 4 a Duniya.
Yanzu haka dai Kasar Iraki ce ta farko a wannan jerin da aka fitar, sannan kuma Kasar Afghanistan. Bayan Najeriya kuma akwai Kasar Syria wanda ta zo na 4 a bana. Kasar Pakistan ce dai ta zo ta 5 a halin yanzu kamar yadda mu ka ji.

Ana fama da rikicin ‘Yan ta’addan Boko Haram da kuma rigimar Makiyaya a halin yanzu a Najeriya Rigimar Makiyaya dai yayi sanadiyyar dinbin mutanen da su ka haura adadin wadanda ‘Yan Boko Haram su ka kashe a shekarar nan.
Sauran kasashen da su ke wannan sahu sun hada da: Somaliya, Indiya, Yemen, Masar da kuma Kasar Philippines wanda ta zo ta 10. Binciken da aka yi dai ya nuna cewa abubuwa su na lafawa a Najeriya a cikin shekarun baya-bayan nan.
A baya kun ji cewa ‘Dan takarar PDP, Atiku Abubakar ya bayyana cewa zai yi wa tsarin kasar nan garambawul, wanda da zarar an yi hakan, Boko Haram za ta rasa tubulin dafawa a Arewacin Kasar.


Published on: December 6, 2018. at: 4:24 pm

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*