Rundunar sojin Najeriya ta sake tura dakarunta cike da kayan aiki domin su kare Jakana, wani gari a karamar hukumar Konduga da ke jihar Borno.
An gano rundunar wanda aka jona da na Operation Lafiya Dole a ranar Laraba, 5 ga watan Disamba cike da kayayyaki da dabarun yaki a Mainok, wani gari yan mil kadan daga Jakana.
Channels TV ta ruwaito cewa jami’an tsaro sun yada zango kusa da wuraren binciken ababen hawa a yankin inda ake ta bincikar matafiya sosai.
Hakan baya iya rasa nasaba da wani rahoto da ke yawo tun a ranar Talata na hare-hare da ake kaiwa kauyukan da ke kewaye da Jakana.
Wani dan jarida Ahmed Salkida ya wallafa a shafin twitter cewa “yan ta’addan Boko Haram sun fara taruwa a kauyen Mattari a karamar hukumar Konduga.
“Wajen na kusa da Jakana ko Benishek, akwai hukumomin sojin Najeriya a yankunan biyu, wasu majiyoyi suka ruwaito hakan.”
Sai dai rundunar sojin bata yi martani akan hakan ba tukuna.
Leave a Reply