Da alama Manchester United ya tabbatar da nadin Ole Gunnar Solskjaer a matsayin kocin rikon kwarya na Old Trafford.
Babu dai wani bayani a hukumance da ke nuna cewa dan wasan dan asalin Norway shi ne zai gaji Mourinho wanda aka kora ranar Talata.
Amma wani shafi na kungiyar ya bayyana tsohon dan wasan gaba na kungiyar a matsayin ‘manajan rikon-kwarya’. Amma daga baya an goge bayanin.
Solskjaer, dan shekara 45, ya zura kwallo 126 a wasannin da ya buga wa Manchester United a kakar wasanni 11 karkashin jagorancin tsohon kocin kungiyar Sir Alex Ferguson.
Yanzu haka shi ne ke horas da wata kungiya mai suna Molde a kasar Belgium, wadanda yanzu haka suke hutu bayan karewar kakar wasanni a kasar.
Wani hoton bidiyo a shafin intanet na kungiyar Manchester United ya nuna Solksjaer a lkacin da ya zura kwallon da ta bai wa kungiyar nasara a karawar karshe na gasar zakarun nahiyar Turai, da kungiyar Bayern Munich a shekarar 1999, inda aka rubuta cewa: “Solskjaer ya zama kociyan rikon-kwarya, kakannin wasa 20 bayan zura wannan kwallo a filin wasa na Nou Camp…”
Firaministar Norway ma Erna Solberg ta yi maraba da nadin na Solskjaer a shafinta na sada zumunta, inda ta rubuta cewa “Wannan babbar rana ce ga wasan kwallon kafa a kasar Norway. Ina maka fatan alheri wajen rike Red Devils.” Ita ma daga baya ta goge bayanin.
Idan nadin ya tabbata, wasan farko da Solskjaer zai buga a matsayin kocin kungiyar shi ne wanda United za ta kara da Cardiff City ranar Asabar.
United na sa ran zabo mai horsa da kungiyar na din-din-din a karshen kakar wasan baba.
Tsohon dan wasan na Norway, Solskjaer na jan ragamar kungiyar Molde ne tun shekarar 2015, a karo na biyu da yake jagorantar wata kungiyar kwallon kafa. A farkon wannan watan ne ma ya sabunta yarjejeniyarsa da kulob din.
A lokacin da yake wasa a United, Solskjaer ya lashe kofunan Firimiya na Ingila sau 6, da na kalubale (FA) guda 2.
Manchester United ce ta 6 a teburin gasar Firimiya, amma sun fi kusa da kasan teburi idan aka kwatanta tazarar maki da ke tsakanin ta da Liverpool, wadda ke saman tebiri, wadda kuma ta lallasa United din da ci 3-1 a ranar Lahadi.
Leave a Reply