Wanda bai ji bari ba: Wani matashin dan luwadi ya gamu da fushin Alkalin babbar kotu

Wata babbar kotun jahar Borno ta yanke ma wani matashin dan luwadi, Abubakar Ali mai shekaru 24 a rayuwa hukuncin dauri na shekaru biyar a gidan yari tare da horo mai tsanani, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Majiyar Legit.comta ruwaito lauya mai kara, Barista Zainab Bukar ta shaida ma kotu cewa suna tuhumar Abubakar wanda ke zama a unguwar Kaleri dake cikin garin Maiduguri da laifin aikata luwadi da wani karamin yaro mai shekaru 13 a ranar 27 ga watan Yuli da misalin karfe 8 na dare.

Lauya Zainab ta cigaba da zayyana ma kotu cewa wani mutumi mai suna Abba Abdullahi, da shima mazaunin unguwar Kaleri ne ya kai karar dan luwadin ga ofishin Yansanda dake Gwange a ranar 27 ga watan Yuli na shekarar 2018.
Bayan sauraron korafin lauya mai kara, sai Alkalin babbar kotun, mai sharia Alkali Wakkil ya bayyana cewa ta tabbata wanda ake kara ya tafka wannan laifi, kuma wannan mummunan laifi ya saba ma sashi na 284 na kundin dokokin hukunta manyan laifuka na jahar Borno.
Haka zalika mai shari Wakkil ya bayyana cewa babu wani addini daya amince da irin wannan mugunyar dabi’a, toh amma a cewarsa, tunda iyayen wanda ake kara da lauyoyinsa sun nemi ayi masa sassauci, zai duba.
“Don haka na yanke masa hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekaru biyar, tare da horo mai tsanani. Da ba don lauyoyinsa da iyayensa sun nemi a masa sassauci ba, da na yanke masa shekaru goma sha hudu.”Inji shi.


Published on: December 14, 2018. at: 4:59 pm

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*