– Wani dan majalisar a jihar Kogi, Mr. Enench ya rasa kujerarsa sakamakon sauya shekarsa daga jam’iyya mai mulki ta APC zuwa jam’iyyar Adawa ta PDP
– Mambobin majalisar da suka halarci zaman majalisar na ranar Talata ne suka kada kuri’a, inda suka amince a bayyana kujerar Mr Enench a matsayin wofi
– Sai dai Mr Enench ya ce sam wannan mataki da majalisar ta dauka ya saba dokar kasar, kasancewar tuni maganar na gaban kotu
Majalisar dokoki ta jihar Kogi, ta bayyana kujerar Hon. Linus Enench, dan majalisar da ke wakiltar mazabar Olamaboro a majalisar dokokin jihar a matsayin wofi wacce babu kowa a kanta.
Majalisar ta yanke wannan hukunci ne a ranar Talata a zaman majalisar da ta yi a Lokoja biyo bayan sauya shekar Enenche daga jam’iyya mai mulki ta APC zuwa jam’iyyar adawa ta PDP.
Enenche ya rasa wannan kujera, biyo bayan wani kuduri da shugaban masu rinjaye na majalisar, Hon, Bello Hassan Abdullahi ya gabatar.
Abdullahi ya gabatar da wannan kuduri nasa ne dangane da wata wasika da shugaban APC na jihar, Mr Abdul Bello ya aikewa majalisar inda yake sanar da ficewar Mr Enenche daga APC zuwa PDP.
Da wannan ne, Abdullahi ya bayyana cewa Enenche ya saba sashe na 109 -1 sakin layi na G da ke cikin kundin tsarin mulkin kasar kamar yadda aka sabunta shi.
Sai dai kakakin majalisar, Hon Mathew Kolawole, bai dauki mataki da hannunsa ba, inda ya bukaci mambobin majalisar su kada kuri’a. Kashi 2 cikin 3 na mambobin majalisar da ke a zaman suka amince da a bayyana kujerar Enenche wofi, wacce babu kowa kanta.
A bangaren Mr Enenche kuwa, ya ce wannan mataki na majalisar ya saba doka kasancewar tuni dama maganar take gaban kotu, yana mai cewa bayyana kujerarsa a matsayin wofi ya sabawa dokar kasar.
Leave a Reply