Yadda na lashe zaben shugabancin kasa na 2015 – Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce gajiya da rashawa da cin hanci da al’ummar Najeriya su kayi a shekarar 2015 na daya daga cikin muhimman abubuwan da sanya ya samu nasarar lashe zaben shugabancin kasa wancan lokacin.
Shugaba Muhammadu Buhari ya ce kazamar rashawa da ya mamaye Najeriya kafin kafuwar jam’iyyar All Progressives Congress APC yana daya daga cikin dalilan da yasa ya yi nasarar lashe zaben 2015.
Shugaban kasar ya yi wannan furucin ne a jawabinsa na bude taron bayar da horo kan rashawa na manyan jami’ai da shugabanin hukumomin yaki da rashawa da ke kungiyar tarayya Afirka da aka gudanar a fadar Aso Villa da ke Abuja.
Shugaba Buhari ya lura cewa rashawa da matsalolin da ta ke haifarwa a sassan kasar ya zama abin damuwa matuka.

Sai dai ya ce gwamnatinsa ta fara daukan matakai domin kawo gaskiya da nagarta a harkokin mulki kuma ba zai kyale duk wanda aka samu yana cin dukiyar al’umma zai fuskanci hukunci.
“A lokacin da muka hau mulki a 2015, rashawa da matsalolin da take haifarwa ya yiwa ‘yan Najeriya katutu kuma duk abubuwa sun tabarbare.
“Nasarar da muka samu a yayin zaben ba zai rasa nasaba da bore da al’umma suka yi saboda mummunar rashawa da ta mamaye kasar.
“A watannin da suka gabata, mun fara daukan matakai domin kawo gyra da tsafta cikin harkokin gwamnati tare da hukunta dukkan wadanda aka samu suna wawushe dukiyar kasa.
“Sai dai, yaki da rashawa da kwato kudaden da aka sace abu ne mai wahala. Duk da cewa mun samu nasarori, rashawar itama tana yaki da mu.
“Saboda makuden kudaden da aka sace, wasu bata gari sun fara yunkurin amfani da kudi domin kawo cikas ga hukumomin tsaro da niyyar kaucewa hukuncin,”inji shugaban kasar.
Ya ce wasu matakan da gwanatinsa ta dauka domin magance rashawa sun hada da lambar asusun banki na BVN, Asusun guda na gwamnati TSA, hadin gwiwa da gwamnati keyi da ‘yan kasuwa da kuma dokoki da dama da aka kafa domin karfafa hukumomin yaki da rashawa.


Published on: December 10, 2018. at: 10:03 pm

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*