Mu da ƙasarmu amma ana nuna mana wariya – Musulman Indiya

 

Shekara shida da suka wuce, wani yaro Musulmi ya koma gida ransa a ɓace daga wata shahararriyar makaranta da ke garin Agra na arewacin Indiya.

“‘Yan ajinmu na kira na ɗan ta’addan Pakistan,” kamar yadda yaron mai shekara tara ya faɗa wa mahaifiyarsa.

Marubuci kuma ƙwararre wajen ba da shawara, Reema Ahmad, na iya tuna abin da ya faru da kyau.

“Yaron ransa ya ɓaci ƙwarai, ya dunƙule hannu da kyau har ma ana iya ganin alamar tabon ƙusa a tafin hannun nasa. Ransa a ɓace yake matuƙa.”

Reema Ahmad ta cire ɗanta daga wata shahararriyar makaranta saboda ‘yan ajinsu na kiran sa da ‘ɗanta’addan Pakistan’

Tun daga lokacin da jam’iyyar Bharatiya Janata Party (BJP) mai tsattsauran ra’ayin addinin Hindu ta Shugaba Nerandra Modi ta ha mulki a 2014, Musulman Indiya miliyan 200 suka shiga wani hali.

‘Yanbangar Hindu sun kashe mutanen da ake zargin suna sayar da naman shanu tare da kai wa wasu shagunan Musulmai hari. An sha kai ƙarar masallatai. Aka dinga nuna matan Musulmai a intanet a matsayin “gwanjo”. Su ma kafofin yaɗa labarai na masu tsattsauran ra’ayi sun taimaka wajen ta’azzara ƙyamar Musulmai ta hanyar zargin aikata “jihadi”, da kuma yi wa maza Musulmi ƙaryar cewa suna sauya wa matan Hindu addinin ta hanyar aure.

Su ma kalaman ƙiyayyar Musulinci sun ƙaru – an fi samun akasarin irin waɗannan lamurra daga jihohin da BJP ke mulki.

“An mayar da Musulmai saniyar-ware, marasa rinjaye a cikin ƙasarsu,” a cewar Ziya Us Salam, marubucin wani sabon littafi mai suna “Being Muslim in Hindu India” – wato Zama Musulmi a Ƙasar Indiya Mai Bin Addinin Hindu.

Amma BJP da Mista Modi na musanta cewa ana muzguna wa marasa rinjaye a Indiya.

“Wannan ya fi faruwa daga mutanen da ba su damu su haɗu da sauran mutane daga al’adu daban-daban ba. Hatta marasa rinjayen na Indiya sun daina yarda da wannan uzurin,” kamar yadda firaministan ya faɗa wa mujallar Newsweek.

A 2019, Reema ta fita daga wani zauren dandalin WhatsApp inda su biyu ne kaɗai Musulmai. Matakin ya biyo bayan harin da Indiya ta kai kan ‘yan gwagwarmaya a yankin Kashmir da ke ƙarƙashin ikon Pakistan.

“Idan suka kawo mana hari da makamai masu linzami, za mu shiga gidajensu mu kashe su,” a cewar saƙon da aka tura zauren, wanda ke jaddada abin da Mista Modi ya taɓa faɗa game da kashe ‘yanta’adda da kuma maƙiya Indiya a cikin gidajensu.

“Na ji haushi. Na tambayi ƙawata me ke damun ki? Kin yarda da kisan yara da fararen hula?” kamar yadda Reema ta bayyana.

“Wata ta tambaya, kina goyon bayan Pakistan ne kawai sabaoda ke Musulma ce? Sun zarge ni da nuna ƙiyayya ga ƙasata,” in ji ta.

“Nan take aka mayar da kiran zaman lafiya a matsayin ƙiyayyar ƙasa. Na faɗa musu cewa ba sai na zama mafaɗciya zan kare ƙasata ba. Sai na fice daga zauren.”

A cewar yaron, ‘yan ajin nasu na tsaka da faɗa na wasa lokacin da wani malaminsu ya fita daga ajin.

“A lokacin ne kuma wani rukunin ɗalibai ya nuna shi kuma suka fara cewa, ‘Wannan ne ɗan ta’addan Pakistan. Ku kashe shi!'”

Ya ce wasu kuma na kiran sa da nali ka kida (ƙwaron cikin kwata). Mahaifiyarsa ta yi ƙorafi amma sai aka faɗa mata cewa “suna raya abubuwan ne a zuci kawai…ba faruwa abubuwan suka yi ba”.

Daga baya ta cire shi daga makarantar. Yanzu yaron mai shekara 16 a gida yake karatu.

“Na lura da irin halin da a’lummarmu ke ciki ganin abin da ya faru da yarona, abu ne da bai taɓa faruwa da ni ba lokacin da nake tasowa a yarintata,” in ji ta.

Wani fasinja ya tambayi Kaleem Ahmed Qureshi a cikin mota ko kayan kaɗe-kaɗen da yake riƙe da su a akwati bindiga ce

Abokan ɗanta sun sha ɗebe kewa a gidanta mai yalwa tsawon lokaci, ba tare da wani bambancin jinsi ko addini ba. Amma yanzu da ake zargin mazan Musulmi da sauya wa matan Hindu addini da kalmar “soyayyar jihadi”, hakan na nufin mata daga cikin abokan nasa za su tafi gida a wani lokaci kuma ba za su shiga ɗakinsa ba.

“Ni da mahaifina mun zauna mun faɗa wa ɗana cewa akwai matsala saboda haka dole ne ya rage yawan abokai, ya kiyaye, ya daina daɗewa a waje sosai. Ba ka sani ba, za a iya zargin ka da yin ‘soyayyar jihadi.'”

Mai rajin kare muhalli Erum, wata mazauniyar Agra, shi ma ya lura da sauyin da aka samu game da hira tsakanin yaran birnin a matsayinsa na malami a makarantun yankin.

“Kada ku kula ni, mahaifiyata ta ce kada na kula ku,” ta ji wani ɗalibi yana faɗa wa wani ɗan ajinsu Musulmi.

Erum ta ce sauyin da aka samu tsakanin yara ya nuna ƙaruwar ‘ƙyamar Musulmi’
“Ina ta tunani, na ce kai da gaske?1 Wannan ya nuna ƙaruwar tsanar Musulmi. Babu mamaki wannan ya zama wani abu da ba za mu iya warkewa daga shi ba cikin sauƙi,” a cewar Erum.
Amma ita tana da ƙawaye ‘yan Hindu masu yawa, amma kuma ba ta jin daɗin sakewa a matsayinta na Musulma.
Ba wai maganar yara ba ce kawai.
A ofishinsa da ke wani titi a Agra, Siraj Qureshi, wani ɗanjarida kuma mai tsara tattaunawa tsakanin addinai, ya koka kan yadda zamantakewa ta lalace tsakanin Musulmai da Hindu.
Ya tuna wani abu da ya faru a kwanan nan, lokacin da wasu masu tsattsauran ra’ayi ‘yan Hindu suka tare wani mutum da ke ɗauke da naman akuya, suka miƙa shi ga ‘yansanda kuma aka kulle shi a gidan yari.
“Yana da cikakken lasisinsa, amma duk da haka ‘yansanda suka kama shi. An sake shi dai daga baya,” a cewar Siraj.
Da yawan Musulmai a yankinkin yanzu sun sauya yadda suke tafiye-tafiye a jirgin ƙasa saboda yadda ake yawan kai musu hari saboda suna ɗaukar naman shanu. “Yanzu a ankare muke gaba ɗaya, sai mu ƙi shiga jirgin ƙasar ma kawai idan za mu iya,” in ji Reema.
Kaleem Ahmed Qureshi injiniya ne kuma makaɗi, wanda ke zaune a Agra.
Wata rana ya shiga tasi tare da wani fasinja ɗauke da kayan kiɗan nasa da aka fi amfani da su a Afghanistan daga Delhi zuwa Agra. “Lokacin da ya ga akwatin, ya nemi na buɗe ta saboda yana tsoron ko bindiga ce a ciki. Na lura cewa ya yi hakan ne saboda ya ji sunana,” a cewar Kaleem.
“Muna cikin zaƙuwa. Idan zan yi tafiya yanzu dole ne sai na yi ta dudduba inda nake, da abin da zan ce, da duk abin da nake yi. Ko sunana ba na jin sauƙin faɗa wa mutane a cikin jirgin ƙasa.”
“Siyasa ta rusa alaƙa tsakanin al’umma,” in ji shi.
Wasu masu rajin kare haƙƙin Musulmi kenan lokacin da suke faman neman haɗin kai a Kolkata a 2022

Wasu masu rajin kare haƙƙin Musulmi kenan lokacin da suke faman neman haɗin kai a Kolkata a 2022
“Babu wani dalilin da zai sa Musulmai su kasance cikin damuwa,” in ji Syed Zafar Islam, mai magana da yawun jam’iyyar BJP, yana mai alaƙanta ƙiyayyar Musulmi da cewa aikin “kafofin yaɗa labarai ne marasa hankali”.
Na tambaye shi irin matakin da zai ɗauka idan ‘ya’yansa suka koma gida daga makaranta suka ce abokansu na ce musu “yanta’addan Pakistan” saboda su Musulmai ne. Sai ya ce:
“Kamar kowane uba, zan ji ba daɗi. Haƙƙin makarantar ne su tabbatar cewa irin waɗannan abubuwan ba su faru ba.”
Yaya batun kafa jihar Hindu da BJP ke faɗa a ƙasar da kashi 79 cikin 100 ta ‘yan Hindun ce?
“Kowa ya san wannan magana ce kawai. Jam’iyyarmu ko gwamnati ta taɓa faɗar hakan? Ranmu yana ɓaci idan kafofin yaɗa labarai na bai wa irin waɗannan maganganu dama,” in ji Syed.
To kuma yaya batun ƙarancin Musulmai a gwamnati? BJP ba ta da wani minista Musulmi, ko ɗan majalisa, sai wani guda ɗaya a majalisar wata jiha daga cikin sama 1,000 a faɗin ƙasar.
Mista Alam, wanda shi ma ɗan majalisa ne, ya ce ba da gangan suka yi hakan ba.
Arzoo Parveen ta yanke shawarar zama likita bayan ɓata lokaci wajen kula da mahaifiyarta ya yi sanadiyyar mutuwarta

Arzoo Parveen ta yanke shawarar zama likita bayan ɓata lokaci wajen kula da mahaifiyarta ya yi sanadiyyar mutuwarta
Abu ne mai wuya a fayyacewa ko abubuwa na yin sauƙi.
Amma gaskiya ne duk da irin wannan rikita-rikita, Musulmai na cewa yankunansu na sauyawa.
“Musulmai na ƙara samun ilimi. Ƙwararru daga Musulmai na ƙara ƙaimi wajen ilimantar da matasan Musulmai mabuƙata. Idan mutum ya ilimantar da kan sa zai taimaka amma dai mutane sun dawo daga rakiyar gwamnati,” a cewar Mista Salam.


Published on: April 30, 2024. at: 6:32 am

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*