Akwai rashin tabbas game da makomar Henderson a Ajax, Liverpool na zawarcin Amoura
Akwai rashin tabas game da makomar dan wasan tsakiya na Ingila Jordan Henderson mai shekara 33 a Ajax bayan da Kungiyar ta kasar Netherlands ta kasa tsallakewa zuwa gasar zakarun Turai a kakar wasanni ta biyu a jere. (Athletic – subscription required)
Rahotanin da ke cewa dan wasan tsakiya na Newcastle Bruno Guimaraes dan shekara 26 zai koma taka leda a Paris Saint-Germain a wannan bazara ba dai- dai bane kuma bangaren kungiyar ta Faransa ba su nuna alamun su na son su dauki dan kasar Brazil ba. (Mail)
Kocin Netherlands Arne Slot na shirin tarewa a gidan Jurgen Klopp da ke Formby idan ya maye gurbin ba Jamushen a matsayin kocin Liverpool. (Mirror)
Watakila Liverpool ta kara inganta tawagarta ta hanyar daukar dan wasan gaba na kasar Algeria Mohammed Amoura mai shekara 24 daga Union Saint-Giloise. (TEAMtalk)
Bayern Munich ta fara tattaunawa da tsohon kocinta Hansi Flick game da komawarsa kungiyar a matsayin kociyanta domin maye gurbinThomas Tuchel. (Sky Germany)
Dan wasan mai kai hari na Faransa Kylian Mbappe, 25, zai kasance dan wasan da aka fi biya a Real Madrid idan ya rattaba hannu kan kwantaraginsa da kungiyar bayan ficewarsa daga Paris Saint-Germain. (RMCsport)
Tafiyar Mbappe za ta sa PSG ta samu raran kudi na yuro miliyan 220 duk da cewa dan wasan mai kai hari ya barte ne a kyauta. (Sky Sports)
Ana samun ci gaba a sabuwar tattaunawar da ake yi tsakanin Barcelona da dan wasan tsakiyarta dan kasar Sfaniya Marc Casado dan shekara 20 tun watan Afrilun daya gabata . (Fabrizio Romano)
Barca na fuskantar adawa daga Arsenal da Juventus wajan cimma matsaya da dan wasan tsakiya na Real Sociedad da Sfaniya Martin Zubimendi mai shekara 25. (Mundo Deportivo – in Spanish)
Dan wasa mai tsaron bayan Scotland Kieran Tierney mai shekara 26, ya ce ga dukan alamu wasansa a Arsenal ya zo karshe bayan ya shafe wannan kaka ya na tamaula a Real Sociedad a matsayin dan wasan da aka bada shi aro. (Athletic – subscription required)
Leave a Reply