BANBANCI DAKE SAKANIN SURFACE, DEEP DA KUMA DARK WEB KO DARK NET A INTERNET
SURFACE WEB: Na nufin shafukan yanar gizo (websites) da ake iya shigarsu a koda yaushe batare da matakala ba (Login) ayi duk abinda ake bukata a fito, irin wadannan misalan shafukan sune irinsu Search Engines (Google, Yandex, DuckDuckGo, Bing, Yahoo Search, Baidu, Ask da sauransu), Encyclopedia (Wikipedia, WikiHow da etc), shafukan Blog da sauransu. Na tabbata kusan dukkanmu masu shiga yanar gizo zaiyi wuya bamusan Google da Wikipedia ba, irin wadannan shafukan idan da zamu lura basa bukatar muyi amfani da Username da Password ko Email da Password dan yin wani abu a shafukan illa dai, dai dai kun waja je. A takaice dukkan shafin da babu Username da Password kafin ka iso bayanan cikinsa su ake kira “Surface Web” wadanda kullum a fili suke.
DEEP WEB: Dukkan shafin da za’a bukaci asaka Email da Password ko Username da Password (Login) kafin a iso muhimman abubuwa dake ciki shi ake kira da “Deep Web”, irin wadannan shafukan a bayyane suke kusan kashi 70% na shafukan mu na yau da kullum da muke amfani dasu sune irinsu Facebook, Twitter da Instagram da sauransu, kusan dai kowa yasansu.
DARK WEB: Gidan barna, na tabbata ko a sunan zamu fahimci cewar shafuka ne na musamman, irin wadannan shafukan na “Dark Web” ba’a ganinsu a Google ko kuma wani Search Engine. Irin wadannan shafukan da ake kira “Dark Web” suna nan a wani bangare na yanar gizo wanda indai mutun yanaso a ziyarcesu to kuwa yana bukatar manhajoji na musamman wadanda zasu iya bude irin wadannan shafukan. Sanannen manhaja daga cikin manhajoji da ake amfani dasu wajen ziyartar shafukan “Dark Web” ana kiransa “Tor Browser”.
Shafukan “Dark Web” mafi yawan lokuta suna amfani da domain ne mai suna “.onion” kuma adireshinsu ya banbanta da irin adireshin shafukan mu na yau da kullum da muke amfani dasu misali ga adireshin wani shafin Dark Web http://www.propub3r6espa33w.onion. Babu irin barnar da ba’ayi a Dark Web kama daga dillancin kwaya, siyar da bayanan mutane, siyar da bayanan kasa, dillancin kisan mutun, cinikin makamai da sauransu. Kuma wasu daga cikin sanannun shafuka da muke amfani dasu yau da kullum sunada reshe a “Dark Web” irinsu Facebook ga kuma adireshinsa
http://www.facebookcorewwwi.onion.
Wani yakan iya cewa menene amfanin shi Dark Web din? Amfaninsa shine babu mai bibiyar abinda kake indai shima ba kwararre bane domin akwai kula da privacy acen ta yadda shafukan basa ajiye bayananka ko kuma manhajar akayi amfani dasu din. Mudai anan mafi yawan wadanda sukafi amfani da shafukan sune “Hackers (Masu harkokin hacking ko dandantsa)”.
Muhammad Baba Goni (Royalmaster)
13-05-2022
Leave a Reply