DAGA PROF: PANTAMI ABUBUWA GUDA GOMA SUNA GOGE ZUNUBAI DA IZININ ALLAH
1. Ka goge shi da Tasbihinka:
Manzon Allah ﷺ ya ce: “Wanda ya ce: Subhanallahi wabi hamdihi acikin wuni sau dari za’a goge zunubansa ko da sun kai yawan kumfar Teku”.
صحيح مسلم
2. Ka goge shi da Istigfarinka:
Manzon Allah ﷺ ya ce: “Wanda ya ce: Astagfirullahal lazii la’ilaha illa huwal Hayyul Qayyum wa’atuubu ilaihi; za’a gafarta masa zunubansa koda ya kasance zunubin guduwa daga fagen daga ne”.
[صححه الألباني]
3. Ka goge shi da wannan Zikirin:
Manzon Allah ﷺ ya ce: “Babu wani akan ƙasa da zai ce: La’ilaha illallahu, Wallahu Akbar, Wala haula Wala Quwwata illa billah, fa ce an kankare masa zunubansa, ko da sun kai yawan kumfar Teku”.
[صحيح الجامع]
4. Ka goge shi bayan gama cin abincinka:
Manzon Allah ﷺ ya ce: “Wanda yaci wani abinci, sannan ya ce: Alhamdu lillahil lazii Aɗ’amanii hazaɗ ɗa’am, warazaƙaniihi min gairi haulin minnii wala Quwwata, za’a gafarta masa abin da ya gabata na zunubansa”.
[صحيح الجامع]
5. Ka goge shi lokacin sanya tufafinka:
Manzon Allah ﷺ ya ce: “Wanda ya sanya tufafi ya ce: Alhamdu lillahil lazii kasanii haza, waraƙaniihi min gairi haulin minnii wala Quwwata, za’a gafarta masa abin da ya gabata na zunubansa”.
[صحيح الجامع]
6. Ka goge shi lokacin kiran sallah:
Manzon Allah ﷺ ya ce: Wanda ya ce lokacin da yaji kiran sallah: Ash’hadu alla ilaha illallahu, wahdahu lasharika lahu, wa anna Muhammadan Abduhu warasuluhu, radhitu billahi rabban, wabi Muhammadan rasulan, wabil Islami diinan, za’a gafarta masa abin da ya gabata na zunubansa”.
[صحيح مسلم]
7. Ka goge shi lokacin Alwala:
Manzon Allah ﷺ ya ce: “Wanda yayi Alwala, ya kyautata Alwala, zunubansa zasu fita daga jikinsa, har sai sun fita ta ƙarƙashin farautansa”.
[صحيح مسلم]
8. Ka goge shi bayan kowace Sallah (ta farillah):
Manzon Allah ﷺ ya ce: “Wanda ya yiwa Allah Tasbihi (Subhanallahi) sau 33, ya yiwa Allah Tahmidi (Alhmdulilillahi) sau 33, ya yiwa kabbara (Allahu Akbar) 33, 99 da kenan sannan ya faɗi cikon na 100: La’ilaha illallah
Leave a Reply