Inna Lillahi Wa Inna Ilaihi Rajiun : Sau ɗaya muke iya cin abinci a rana'

 Inna Lillahi Wa Inna Ilaihi Rajiun : Sau ɗaya muke iya cin abinci a rana’

Ƙila mu ci abinci a daren nan, ba dai gobe ba,” a cewar wata uwa a Sudan, Madina Yahya.
Madina na magana ne kan yanayin rayuwa a El Fasher, babban birni a yankin Arewacin Darfur da ke Sudan.
Ban da ‘yan kwanakin nan, ana kallon birnin a matsayin tudun tsira. Wannan ya sa Madina da iyalanta suka koma can daga ƙauyensu saboda ba su da tabbacin samun abinci da tsaro.
Amma yanzu saboda birnin na ƙarƙashin kulle da dakarun Rapid Support Forces (RSF) da suka yi, Madina da sauran dubban mazaunansa na faman neman yadda za su tsira da rayuwarsu.
Yayin da yaƙi tsakanin RSF da dakarun sojin Sudan ke ƙara ƙamari, El Fasher ne babban birni na ƙarshe da ke ƙarƙashin ikon gwamnatin ƙasar.
Birnin na da al’umma kusan miliyan 1.5, waɗanda suka haɗa da ƴan gudun hijira 800,000 da suka gudu daga gidajensu saboda yaƙin. Daga abubuwan da birnin El Fasher ya shahara da su akwai hedikwatar sojin Sudan, da kuma cibiyar kasuwanci tsakanin ƙasar da Libya da Chadi.
Bayan ɓarkewar ƙazamin faɗa a ranar Juma’a, ana fargabar mutum 160 aka raunata.
A ranar Lahadi kuma, ƙungiyar bayar da agajin lafiya ta RSF ta ce an kashe aƙalla yara biyu tare da raunata wasu bayan wani bam ya faɗa kusa da asibitin yara. Ba a san wanda ya kai harin ba zuwa yanzu.
Yayin da RSF ke ƙara matsawa, ƙwararrun Majalisar Ɗinkin Duniya na fargabar “mummunar ɓarna” kan fararen hula da suka maƙale a cikin birnin ba tare da sanin hanyar tserewa ba.
Yaƙin shekara guda
Tun watan Afrilun 2023, Sudan ta shiga cikin rikici tsakanin RSF, ƙarƙashin jagorancin Janar Mohamed Hamdan “Hemedti” Dagalo, da kuma sojojin gwamnati ƙarƙashin Janar Abdel Fattah al-Burhan.
Janar-janar ɗin sun kasance abokai a baya lokacin da aka kifar da gwamnatin Omar al-Bashir a juyin mulkin 2019. Sai dai rashin fahimta game da yi wa rundunar tsaron ƙasa kwaskwarima da kuma kafa gwamnatin riƙon kwarya ya farraƙa su, har ma suka shiga yaƙar juna.
Tashin hankalin da ya faro daga birnin Khartoum ya karaɗe ƙasar cikin sauri, zuwa Arewacin Kordofan, da kuma zuwa Gezira.
A cewar MDD, an kashe aƙalla mutum 15,000 tun bayan fara yaƙin. Sai dai wakilin musamman na Amurka a Sudan, Tom Perriello, ya ce adadin mutanen zai iya kaiwa 150,000.
‘An kashe min mutane da yawa’
..

Muna fama da ƙarancin abinci,” in ji Shamu Abker, wanda ɗan asalin garin Tawila ne da ke yamma da Elfasher.

“Akasari sau ɗaya muke cin abinci a rana, shi ne na safe,” a cewarsa.
Luguden wuta ya tilasta masa guduwa daga ƙauyensu da ƴaƴansa. Yayin da suke tsaka da tafiya a kan ƙananan tituna don guje wa shingen sojoji, an kashe ɗansa ɗaya a hatsarin mota. Shi ma Shamu ya rasa idanunsa saboda rashin kulawar likitoci.
“Na rasa mutane da dama saboda yaƙin nan, ba zan ma iya lissafa su ba,” a cewarsa.
“Ina kewar natsuwar da na rasa a gidana, Yanzu ina zaune ne a ƙarƙashin bishiya, ƙarƙashin tantin nan ina kewar gidana.”
Madina Yahya ta isa El Fasher ne tare da iyalanta wata shida da suka wuce, kuma ita ma ta bayyana irin wannan yanayi.
“Yaranmu na cikin wannan zaluncin. Mun gaji da wannan lamari,” in ji ta.
A sansanin ƴan gudun hijira, ta lura da yadda masu neman agaji da masu bayar da shi ke fama. Ta ce duk sabon zuwa ana kallon su ne a matsayin ɗawainiya saboda ƙarancin kayayyaki.
“Suna ta kwatanta mu da tsofaffi ko sababbi kamar wani wake,” a cewarta game da yadda ake siffanta sababbin zuwa.
“Ba su iya taimaka mana. Mun rasa gidajenmu duka, amma kuma sai su yi ta ware sababbi da tsofaffi.”
Madina ta kuma bayyana matsalolin da ƴaƴanta mata ke ciki.
“Muna da yara mata masu tasowa. Akwai ƙananan yara da ke shirin balaga kuma suna buƙatar abubuwan da ba za mu iya ba su ba, saboda haka wannan zai ba wa wasu damar su zalunce su.”
Ban da luguden wutar, da hatsaniya, da kisan azarɓaɓi, da sata da ƙone-ƙonen da aka dinga yi, MDD da sauran ƙungiyoyi sun gano kuma yadda ake cin zarafin mata da ƙananan yara.
“Dakarun RSF da ƙawayensu sun aikata fyaɗe mai yawa da sauran laifukan yaƙi,” a cewar rahoton ƙungiyar kare haƙƙin bil’adama ta Human Rights Watch a watan Agustan 2023.
‘Babu zaman lafiya’

Abu ne mai wuya ga fararen hula su samu kayan agaji a Darfur

Fararen hula a Darfur kan ce suna zaune cikin fargaba a kodayaushe, ba su da wurin zuwa ko kuma hanyar samun agaji.

Ƙungiyar bayar da agaji Oxfam ta ce ƴan gudun hijira na cikin barazanar sacewa.

“Fararen hular da ke zaune a birnin sun fito ne daga kusan dukkan sassan Darfur. Kusan akwai mutanen da abin ya shafa daga kowane dangi, Larabawa da ƴan Afirka, idan ɓangarorin na kai hare-hare,” a cewar Toby Harward, wani mai rajin kare haƙƙin bil’adama.

Yayin da ake ci gaba da fafatawa kan iko da El Fasher, babu wasu alamun tsagaita wuta.

“Ba za a yi wata tattaunawa ba, ba zaman lafiya, babu tsagaita wuta har sai an daƙile wannan tawayen,” in ji babban kwamandan sojin Sudan al-Burhan ranar 7 ga watan Mayu.

Duk da yunƙurin Saudiyya, da ƙungiyar ƙasashen Gabashin Afirka IGAD, da Tarayyar Afirka, da Amurka har yanzu ba a iya cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ba.

A cewar ofishin agaji na MDD, sama da kashi ɗaya cikin uku na al’ummar Sudan na fuskantar barazanar yunwa, sannan miliyan 8.7 sun gudu daga muhallansu.


Published on: May 15, 2024. at: 1:05 pm

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*